Hanan al-Ahmadi: Tarihin mace ta farko da aka naɗa a Majalisar Shura ta Saudiyya

Asalin hoton, Alarabiya
A ƙarshen makon jiya ne Sarki Salman na Saudiyya ya naɗa Dr. Hanan Bint Abdulrahim bin Nutlaq al-Ahmadi a matsayin mace ta farko da za ta riƙe muƙamin mataimakiyar shugaban Majalisar Shura.
A Saudiyya, ƴan majalisar Shura ne ke da alhakin gabatar da dokoki domin amincewar masarauta.
Naɗin nata ya zo ne yayin wasu sauye-sauye da Sarki Salman ya aiwatar a manyan hukumomin ƙasar, waɗanda suka haɗa da Majalisar Shura da sauran harkokin addini.
Kazalika naɗin nata zai iya yin tasiri kan yadda ake tafiyar da harkokin mata a ƙasar da ke da tsauraran matakai a kansu.
Wace ce Hanan al-Ahmadi?
An haifi Dr. Hanan Al-Ahmadi a yankin Makkah Al-Mukarramah, kuma Farfesa ce a fannin kiwon lafiya a Makarantar Koyar da Harkokin Mulki ta Saudiyya.
Ta kammala digirinta na farko a fannin Kimiyyar Gudanarwa daga Sashen Tsimi da Tanadi na Jami'ar Sarki Saud a 1986.
Kazalika ta yi Digirinta na Masters a fannin Gudanawar Harkokin Lafiya a Kwalejin Koyar da Manyan Digiri daga Jami'ar Tulane da ke Amurka a 1989.
Dr. Hanan Al-Ahmadi ta kammala Digirin Digirgir a fannin Gudanawar Harkokin Lafiya a Jami'ar Pittsburgh ta Amurka a 1995, inda ta samu lambobin yabo daga ofishin jakadancin Saudiyya da ke Amurka kan bajintar da ta yi a Digirinta na Masters da na Digirgir.
Dr. Hanan Al-Ahmadi ta rike muƙamai da dama a Saudiyya a ayyukan da ta yi a fanonni daban-daban masu muhimmanci.
Ta yi aiki a matsayin shugabar mata a fannin gudanarwa kan harkokin lafiya ta Makarantar Koyar Da Harkokin Gudanarwa daga 2004 zuwa 2008.
Kazalika, ta rike mukamin babbar jami'a a reshen mata na Makarantar Koyar Da Harkokin Gudanarwa daga 2008 zuwa 2009, da kuma tsakanin 2009 zuwa 2012.
Sannan ta rike mukamin Darakta Janar ta reshen mata na Makarantar Koyar Da Harkokin Gudanarwa, inda a 2012 aka naɗa ta a matsayin mamba a Majalalisar Shura.
Aikin Majalisar Shura ta Saudiyya
Majalisar Shura, majalisa ce da ke bayar da shawara ga Sarkin Saudiyya. Ba ta da karfin iko na zartar da hukunci.
Aikinta shi ne gabatar da shawarwari ga sarkin Saudiyya da kuma majalisarsa. Ba za ta iya tursasa wa mutane su bi doka ba, saboda hakan nauyi ne da ya rataya a kan Sarkin.
Majalisar ta Shura tana da mamba 150 kuma sarki ne yake nada dukkansu.
Tun shekarar 2013, Majalisar ta sanya mata 30 a matsayin mambobinta.











