Alamun da ke nuna Saudiyya da Isra'ila sun kusa shiryawa

Palestinians in Gaza protest against Saudi Crown Prince Mohammed bin Salman, Donald Trump and Israel (April 2018)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ƙashen Larabawa na ci gaba da ƙulla ƙawance da Isra'ial
    • Marubuci, Daga Frank Gardner
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC Kan Tsaro

Za su yi ko ba za su yi ba? Wannan ce tambayar da ke zuciyar mutane da dama a Gabas Ta Tsakiya a yanzu haka.

Ko Sarakunan Saudiyya, waɗanda a tarihi aka san cewa masu adawa da Isra'ila da yadda take tafiyar da Falasɗinawa ne, sun kusa gyara dangantakarsu da ƙasar, wacce a baya ƙasashen Larabawa ke alaƙantata da masu aƙidar Yahudanci?

Jita-jitar da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta a baya-bayan nan ta samo asali ne bayan wata hira da tsohon shugaban hukumar leƙen asiri ta Saudiyya Bandar Bin Sultan al-Saud da gidan talabijin na Al-Arabiya, inda ya ragargaji shugabannin Falasɗinu kan sukar yarjejeniyar zaman lafiyar da ake ta yi kwanan nan tsakanin Isra'ila da ƙasashen Larabawa.

''Wannan ba shi ne abin da muka tsammaci ji daga jami'an da suke neman haɗin kan ƙasashen duniya kan fafutukarsu ba,'' a cewar Yarima Bandar, a hirar mai ɓangarori uku.

''Zafin kan da (shugabannin Falasɗinu) suka nuna wa shugabannin ƙasashen yankin Gulf kan wannan abu da ke faruwa lamari ne da ba za a yarda da shi ba.''

Da fari shugabannin Falasɗinu sun bayyana shiryawar da Ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Bahrain suka yi da Isra'ila a matsayin ''cin amana'' da tamkar ''caka musu wuƙa a baya.''

Yarima Bandar, wanda ya shafe shekara 22 a matsayin jakadan Saudiyya a Amurka kuma aboki ne na kusa ga Shugaba George W Bush, inda har ake masa laƙabi da Bandar Bin Bush, ya yi magana kan yadda shugabanci a Falasɗinu ya dinga cin karo da tasgaro a tarihi. Ya shaida wa masu sauraro cewa Falasɗinu ba ta ɗaukar Saudiyya da muhimmanci.

Prince Bandar Bin Sultan Al-Saud

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yarima Bandar ya ce shugabannin Falasɗinawa ba su yi abin a zo a gani ba

Duk da cewa ya yi wata magana da ya kira fafutukar Falasɗinu da ''ɗaya ce kawai'', ya ɗora irin laifin ga shugabannin Isra'ila da Falasɗrinu na kasa cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsawon shekaru.

Ya danganta rabuwar kawuna da aka samu tsakanin hukumomin Falasɗinu da ke shugabantar Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da Ƙungiyar Hamas, mai iko da Gaza, da Falasɗinawa za su iya cimma yarjejeniya ta adalci a yayin da shugabanninsu ba su yarda da junansu ba?

Wani jami'in Saudiyya mai alaƙa da gidan sarautar ƙasar ya ce ba za a sanya irin waɗannan kalaman a gidan talabijin na Saudiyya ba tare da amincewar Sarki Salman da yarima mai jiran Mohammed Bin Salman ba.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An samu sauye-sauye masu tsauri a Saudiyya a 'yan shekarun nan

Jami'in ya ce, zaɓar Yarima Bandar wanda ƙwararre ne kan diflomasiyya kuma wani ginshiƙin Masarautar Saudiyya ya faɗi abin da ya ce ɗin, alama ce mabayyaniya da ke nuna cewa Saudiyyan na shirin cimma yarjejeniya da Isra'ila a ƙarshe.

Camfe-camfe a tarihi

Alamu na nuna cewa da kalaman Yarima Bandar da kuma goyon bayan shiryawar da UAE da Bahrain suka yi da Isra'ila a asirce, na nuna Saudiyya na daf da ƙulla nata ƙawancen ne da Isra'ila.

Tsawon shekaru da suka gabata, musamman ma a yankunan karkara da ke ƙuryar masarautar, ƴan Saudiyya sun taso da aƙidar kallon Isra'ila a matsayin masu ƙiyiya da aƙidar Yahudanci.

Na tuna wata rana a wani ƙauye da ke kan tsauni a yankin Asir, wani ɗan Saudiyya ke gaya min da iyakar gaskiyarsa cewa ''wata rana a wata shekara Yahudawa sun sha jinin jarirai.''

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Saudiyya na daga cikin ƙasashen da aka fi yawan amfani da intanet a yankin Gabas Ta Tsakiya

Godiya ga intanet da tauraron ɗan adam, don yanzu irin waɗannan camfe-camfen sun ragu sosai a ƙasar; a yanzu ƴan Saudiyya na shafe lokaci mai yawa a kan intanet ta yadda suke ƙara sanin duniya da abin da ke faruwa a cikinta.

Sai dai har yanzu akwai sauran aiki kan magance ƙin jinin baƙi da zargin waɗanda ba ƴan ƙasar ba da ke rayuwa a can, wanda tarihi ya nuna an daɗe ana yi, kuma hakan ne ya sa ake ganin shi ya sa mahukuntan Saudiyya ba su yi gaggawar bin sahun takwarorinsu na yankin Gulf ba wajen shiryawa da Isra'ila.

Goyon bayan Saddam

Dangantakar Falasɗinawa da Saudiyya da sauran ƙasashen yankin Gulf mai cike da sarƙaƙiya ce.

Gwamnatocin ƙasashen yankin Gulf sun goyi bayan fafutukar Falasɗinu a siyasance da kuma nauyin aljihunsu a tsawon shekaru.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An kori Faladinawa daga Kuwait saboda goyon bayan da Yasser Arafat ya bai wa Saddam Hussein

Dangantakar Falasɗinawa da Saudiyya da sauran ƙasashen yankin Gulf mai cike da sarƙaƙiya ce.

Gwamnatocin ƙasashen yankin Gulf sun goyi bayan fafutukar Falasɗinu a siyasance da kuma nauyin aljihunsu a tsawon shekaru.

Amma a lokacin da shugaban Falasɗinu Yasser Arafat ya goyi bayan shugaban ƙasar Iraƙi Saddam Hussein kan mamyar da ya yi wa Kuwait a shekarar 1990, sai suka ji tamkar cin amanarsu ya yi.

Bayan hare-haren da aka kai mai taken Operation Desert Storm wanda rundunar sojin haɗaka da Amurka ke jagoranta ta kai da kuma ƙwato Kuwait a 1991, sai ƙasar ta kori dukkan Falasɗinawa da ke can, tare da maye gurbinsu da dubban Misirawa.

A lokacin da na kai ziyara birnin Kuwait da ke cikin ɗimuwa a wannan shekarar, na ga wani rubutun Larabci da aka yi wanda aka yaɗa shi a gefen wani wajen sayar da abinci.

An rubuta "Al-Quds da'iman lil'Sihyouneen, w'ana Kuwaiti.'' Wato "Birnin Ƙudus ne gida na har abada ga Yahudawa, ni kuwa ɗan Kuwat ne.''

An ɗauki tsawon lokaci kafin tsofaffin shugabannin yankin su fita daga ɗimuwar cin amanar da Yasser Arafat ya yi musu.

Wanda ya yi dukkan ƙoƙari don magance wannan matsala da daidaita lamura tsakanin ƙasashen Larabawa ba wani ba ne face shugaban Kuwait, marigayi Sarki Sheikh Sabah al-Ahmad al-Sabah, wanda ya mutu a watan da ya gabata, yana da shekara 91.

Yarjejeniyar zaman lafiya ta Saudiyya

Saudiyya na da tarihi idan aka zo batun kawo ƙarshen rashin jituwa tsakaninta da Isra'ila.

A watan Maris ɗin 2002, na halarci wani taron ƙasashen Larabawa a Beirut, inda wani mutum mai sanƙo da ke Turanci mai kyau, ya yi bayani kan abin da ya kira Shirin Yarjejniyar Zaman Lafiya na yarima mai jiran gado Abdullah.

Mutumin ba wani bane, baya ga Adel Jubair, mai bai wa ofishin yarima mai jiran gado shawara kan harkokin waje na wancan lokacin, wanda a yanzu shi ne ƙaramin ministan harkokin wajen Saudiyya.

UAE Foreign Minister Abdullah bin Zayed (left); Bahrain Foreign Minister Abdullatif Al Zayan (2nd left); Israeli Prime Minister Benjamin Netanyahu and US President Donald Trump at the White House (15/09/20)

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Kasashen Larabawa na ta shiryawa da Israila a baya-bayan nan

Shirin zaman lafiyar ne ya mamaye taron wannan shekarar, kuma dukkan ƙasashen Ƙungiyar Larabawa sun goyi bayan hakan.

Shirin ya bai wa Isra'ila damar shiryawa da dukkan ƙasashen Larabawa kan sharaɗin za ta janye daga dukkan yankunan da ta mamaye da suka haɗa da Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da Zirin Gaza da Tuddan Golan da Labanon.

Tare da bai wa Falasɗinawa Gabashin Birnin Ƙudus a matsayin babban birninsu, da kuma samar da mafita ga ƴan gudun hijirar Falasɗinu, waɗanda yaƙin Larabawa da Isra'ila na shekarar 1948 zuwa 1949 ya shafa, da aka kora daga gidajensu inda a yanzun nan ce ake kira Isra'ila.

Shirin ya samu goyon bayan ƙasashen duniya, ya kuma tursasa Fira Ministan Isra'ila Ariel Sharon amincewa. A nan, a ƙarshe dai, kamar an samu dama ta kawo ƙarshen rikicin Larabawa da Isra'ila na tsawon lokaci.

Jim kaɗan kafin a wallafa shirin, sai ƙungiyar Hamas ta sanya bam a otel ɗin Netanya, inda mutum 30 suka mutu tare da raunata fiye da mutum 100.

Daga nan sai aka dakatar da duk wata tattaunawar zaman lafiya.

Bayan shekara 18 Gabas Ta Tsakiya ta samu ci gaba ta hanyoyi da dama, duk da cewa dai Falasɗinawa har yanzu ba su kai ga samun ƴancinsu ba sannan Isra'ila na ci gaba da mamayar yankunan Falasɗinu da Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, wanda a ƙarƙashin dokar ƙasashen duniya ba ya kan ƙa'ida.

Da UAE da Bahrain da Jordan da Masar a yanzu duk sun gyara dangantakarsu ta diflomasiyya da Isra'ila ta hanyar cimma yarjejeniya.

A taƙaice dai, ba kamar irin yarjejeniyar da Jordan da Masar suka yi da Isra'ila a bisa tursasawa ba, a yanzu ƙasashen biyu suna daf da cimma yarjejeniya mai kyau da Isra'ilar.

Taka tsantsan

To ko yaya jami'in Isra'ila ke ji dangane da yiwuwar shiryawa da Saudiyya?

Tabbas sun kalli hirar da aka yi da Yarima Bandar amma har yanzu sun ƙi cewa komai kai tsaye.

A maimakon haka, sai wani mai magana da yawun ofishin jakadancin Isra'ila ya ce: ''Muna fatan wasu ƙasashen da dama za su fahimci abin da ke faruwa a Gabas Ta Tsakiya su ma su biyo turbar sasanci.''

Saudiyya na bin komai a hankali kan duk abin da ya shafi sauya tsare-tsare, ta hanyar gwada kowane yunƙuri kafin ta ba da kai bori ya hau.

Amma isowar Yarima Salman mai tafiya da zamani wannan fage ya sauya yadda abubuwa ke tafiya a baya.

A yanzu mata na tuƙa mota, ana harkokin shaƙatawa, kuma ƙasar tana bai wa masu yawon buɗe ido damar zuwa.

Don haka yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Saudiyya da Isra'ila, a yanzu wani abu ne da zai iya yiwuwa.