Abu biyar da suka sa sulhu tsakanin Isra'ila da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Bahrain yake da muhimmanci

Israeli National Security Adviser Meir Ben-Shabbat elbow bumps with an Emirati official at Abu Dhabi airport in the United Arab Emirates (1 September 2020)

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Mai ba da shawara kan harkokin tsaro a Isra'ila na cikin jirgin da ya tashi zuwa UAE ranar 1 ga watan Satumba
    • Marubuci, Daga Jeremy Bowen
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Editan BBC a Gabas Ta Tsakiya

Manyan wakilai daga Isra'ila da Hadaddiyar Daular Larabawa UAE sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya da Amurka ta shiga tsakani a Fadar White House ranar Talata.

Ministan harkokin wajen Bahrain ya halarci taron tare da sanya hannu kan nata yarjejeniyar don daidaita alakarta da Isra'ila, kamar yadda Shugaba Donald Trump ya sanar a makon jiya.

Wannan shi ne dalilan da ya sa ma'amaloli suke da muhimmanci.

1. Ƙasashen Larabawa na gani za su samu damarmakin cinikayya

Yarjejeniyar ta taimaka wa jama'ar UAE waɗanda suka gina kansu a harkar soji sannan a matsayin wani waje na yin kasuwanci ko kuma zuwa hutu.

Amurkawa ta taimaka wajen ƙulla yarjejeniyar da alƙawarin samar da manyan makamai waɗanda a baya da ƙyar UAE take iya samu. Sun haɗa da jirgin yaƙi ƙirar F-35 da kuma EA-18G.

Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta yi amfani da dakarunta da ke Libya da Yemen. Amma babbar abokiyar gabarta ita ce Iran a wani ɓangaren gaɓar tekun.

US Presidential Adviser Jared Kushner speaks in front of an air-plane of El Al at the Abu Dhabi airport

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jared Kushner, surukin Shugaba Trump, ya taka muhimmiyar rawa a wannan lamari.

Isra'ila da Amurka su ma kamar UAE ba su yarda da Iraniyawa ba. Haka ma Bahrain. Har zuwa shekarar 1969 Iran tana iƙirarin Bahrain a yankinta take. Sarakunan Bahrain su ma suna kallon wani ɓangaren mabiya mazhabar Shi'a a matsayin ƙungiyar Fifth column ga Iran.

Duka ƙasashen Gulf sun ɓoye ƙawancensu da Isra'ila. Suna fatan yin cinikayya a bayyane; Isra'ila na da ɗaya daga cikin manyan fannonin fasaha ta duniya.

Kafin lokacin korona, 'yan Isra'ila na son hutu waɗanda suke zuwa hamada da bakin teku da manyan shagunan yankin tekun Fasha. Kasuwanci ne mai kyau.

2. Isra'ila ta rage keɓe yankinta

Daidaita alaƙa da UAE da Bahrain babbar nasara ce ga 'yan Isra'ila.

Firaminista Benjamin Netanyahu ya yi imani da dabarun da aka fara amfani da su a shekarun 1920 na "Iron Wall" tsakanin ƙasar Yahudawa da Larabawa.

Abin shi ne ƙarfin da Isra'ila ke da shi zai sa Larabawa su gano cewa zaɓin da suke da shi shi ne amincewa da wanzuwarta.

Isra'ilawa ba ta son keɓewar da ake yi mata a Gabas ta Tsakiya. Zaman lafiya da Masar da Jordan bai taɓa zuwa cikin sauƙi ba.

Ƙarfafa ƙawance don yaƙar Iran wata babbar nasara ce. Mista Netanyahu na ganin Iran a matsayin babbar abokiyar gabar Isra'ila, a wasu lokutan tana kwatanta shugabanninta da 'yan Nazi. Ya yi shiru kan korafinsa na asali game da yiwuwar sayen makamai na Hadaddiyar Daular Larabawa.

Shi ma Mista Netanyahu yana cikin rudani, yana fuskantar shari'a kan cin hanci da rashawa da ka iya kai shi ga zaman gidan yari. Ya soma kula da cutar korona yadda ya kamata daga bisani kuma labari ya sha bamban. Masu adawa suna gudanar da zanga-zanga a wajen gidansa da ke Kudus.

3. Donald Trump na bikin juyin mulkin a manufofin ƙasashen waje

Yarjejeniya na aiki a matakai daban-daban ga Shugaban Amurka.

Babban ci gaba ne ga dabarunsa na "matsin lamba" kan Iran. Har ila yau, abu ne mai muhimmanci musamman a shekarar gudanar da zaɓe ya goyi bayan alfaharin da yake yi cewa shi ne babban mai shiga tsakani wajen ƙulla yarjejeniya.

Donald Trump after announcing that Israel and the UAE have agreed to normalise relations (13 August 2020)

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Donald Trump ya sanar da "Yarjejeniyar Abraham" a fadar White House a watan Agusta

Duk wani abu da ya yi yana amfanar Isra'ila ko ma gwamnatin Benjamin Netanyahu, ya yi daidai da masu zaɓe Kirista wani muhimmin ɓangare na magoya bayansa.

Ya kamata ƙawancen "Ƙawayen Amurka" kan Iran su yi aiki yadda ya kamata idan Larabawan yankin Gulf za su bayyana lamuransu maimakon ɓoye-ɓoye kan alaƙarsu da Isra'ila.

Abin da Shugaba Trump ke kira "Yarjejeniyar ƙarni" don samar da zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinawa ba lalle ya tabbatu ba.

Amma "Yarjejeniyar Abraham", kamar yadda aka san yarjejeniyar Isra'ila da UAE, wani gagarumin sauyi ne ga daidaiton iko a Gabas ta Tsakiya kuma Fadar White House ta gabatar da shi a matsayin babban juyin mulkin manufofin ƙasashen waje.

4. Falasɗiwa na ganin an yaudare su

Sun bayyana Yarjejeniyar Abraham a matsayin cin amana. Sabuwar yarjejeniyar ta kawo ƙarshen yarjejeniya da Larabawa suka cimma abin da ke nufin alakar da ake da ita da Isra'ila ita ce samar da 'yanci ga Falasɗinawa.

Amma yanzu Isra'ila na gyara alakar jama'a da kasashen Larabawa yayin da Falasɗinawa har yanzu suke cikin zulumi a karkashin mamayar da aka yi a gabashin Kudus da Yammacin Gabar Kogin Jordan, abin da ya kai ga buɗe gidan yari a Gaza.

Yarima mai jiran gado na Abu Dhabi, Mohammed bin Zayed Al Nahyan, mai rikon kwarya na UAE, ya ce farashinsa ga yarjejeniyar shi ne yarjejeniyar Isra'ila ta dakatar da mamayar wasu sassan Yammacin Gabar Kogin Jordan.

Palestinian Authority President Mahmoud Abbas puts his hand on his head during a meeting of the Palestinian leadership (18 August 2020)

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Shugabannin Falasɗinu sun yi watsi da yunƙurin ƙasashe biyu na yankin Gulf na daidaita alaƙa da Isra'ila

Amma Firaminista Netanyahu ya yi kamar ya ja da baya ga ra'ayin, a yanzu saboda matsin lambar kasashen duniya.

Firgicin Falasɗinawa zai karu yanzu da Bahrain ta shiga yarjejeniyar.

Hakan ba zai taɓa faruwa ba, ba tare da amincewar Saudiyya ba. 'Yan Saudiyya su ne kan gaba a shirin wanzar da zaman lafiya da ke neman a bai wa Falasɗinawa 'yanci.

Matakin Sarki Salman a matsayin mai kula da wurare mafi tsarki biyu a addinin musulunci ya ba shi babban iko. Abu ne da ba lalle ya san da Isra'ila ba.

Ɗansa da magajinsa, Mohammed bin Salman, na iya sakin jiki.

5. Iran na da sabon ƙalubale

Gwamnatin Iran ta yi tur da yarjejeniyar.

Yarjejeniyar Abraham ta sanya su cikin ƙarin damuwa.

Takunkumin da Shugaba Trump ya sanya tuni ya haifar da matsalar tattalin arziki. Yanzu suna da wani ciwon kan.

Iranian students burn Israeli flags during a protest outside the UAE embassy in Tehran, Iran (15 August 2020)

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Yarjejeniyar UAE da Isra'ila ta janyo zanga-zanga a Iran

Sansanonin jiragen saman yakin Isra'ila sun yi wa Iran nisa. Hadaddiyar Daular Larabawa na gefen da ruwan Gulf. Hakan na da matuƙar muhimmanci idan aka dawo batun maganar kai hare-hare ta sama kan wuraren nukiliyar Iran.

'Yan Iran din sun gano cewa an rage musu damar yin wasu dabaru.