Saudiyya ta yi gum a kan matakin Bahrain na farfado da alaka da Isra'ila

Asalin hoton, Reuters
Firai ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana sanarwar Bahrain ta farfado da alakarta da kasarsa a matsayin wata alama ta wanzuwar "sabon zamani mai cike da zaman lafiya''.
Wakilin BBC yace, Falasdinawa sun yi Allah wadai da matakin da suka kira a matsayin "cin amanarsu'', suna kallon hakan a matsayin saba alkawarin da suka yi musu na kin farfado da alaka da Isra'ila har sai an cimma manufar samar da kasa mai zaman kanta ga Falasdinawa.
Kungiyar Hamas ta kira yarjejeniyar a matsayin abar kyama.
yayin da Masar ke maraba da ita, ita kuwa Turkiyya ta yi matukar fusata, harma ta yi barazanar yanke alaka da Bahrain dungurungum.
Har kawo yanzu kasar Saudiyya bata bayyana matsayarta a kan batun ba.

Asalin hoton, Reuters
Da yake sanar da yarjejeniyar, Shugaba Trump ya bayyana ta a matsayin "wata gagarumar nasara da tarihi bai zai mance ba".
Shugaban Amurka Donald Trump ne ya gabatar da shirin na zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya a watan Janairu wanda ke da zummar sulhunta Isra'ila da Falasdinu.
Sannan ya shige gaba wajen kulla dangantaka tsakanin kasashen biyu da Isra'ila.
Mista Trump ya bayyana farin cikinsa, dangane da yadda wasu kasashen larabawa suka karbi shirin hannu bibbiyu, ko da yake wandada ake yi domin su wato Falasdinawan na ci gaba da tur da ita.
"Yau an sake kafa tarihi!" a cewar Mr Trump, inda ya kara da cewa: "Manyan abokanmu biyu Isra'ila da Bahrain sun amince da yarjejeniyar zaman lafiya."
Bahrain ta zama kasar Larabawa ta hudu a Gabas Ta Tsakiya da ta amince da Isra'ila tun kafuwarta a 1948. Sauran kasashen su ne Masar da Jordan.











