An gano wata 'fadar alfarma' da ta yi shekara 2,500 a Birnin Kudus

Asalin hoton, EPA
Masana ilimin kufai sun gano abin da suka bayyana da katafariyar 'fadar alfarma' tun zamanin Daular Yahudawan Bilical a Birnin Ƙudus.
Manyan zane da aka yi a cikin duwatsu da wasu ɓagaruzai da ke da alaƙa da ginin an gano su a wani yanki mai nisan kilomita uku daga kudancin tsohon Birnin Ƙudus.
Masanan sun ce wasu daga cikin abubuwan tarihin an binne su cikin yanayi na adanawa, ko da yake ba su san dalilin hakan ba.
Ana dai tunanin an gina masarautar tun a ƙarni na bakwai zuwa takwas kafin haihuwar Annabi Isa AS.
Cikin abubuwan da ka gano akwai wadanda yanzu ake amfanin da su a Gabashin Talpiot mai makwabtaka, da kuma ake kira Armon Hanatziv.
"Kayayyakin tarihin da ake alaƙanta su da sunayen sarauta ko wurin bautar farko tsakanin karfi na (10 zuwa 6 kafin haihuwar Annabi Isa), sun kasance mafi kayatarwa da burgewa da aka taɓa ganowa zuwa yanzu," a cewar sanarwar mahukunta kan abubuwan tarihi na Isra'ila. Israel Antiquities Authority (IAA).

Asalin hoton, EPA
IAA ta nuna "farin cikinta" cewa biyu daga cikin manyan kayayyakin uku an gano yadda ake binne su a adane, ɗaya kan ɗaya.''
"A wannan gaɓar abu ne mai wahala a ce ga wanda ya ɓoye waɗannan kayan kamar yada aka gano su, da kuma dalilan yin haka," a cewar Farfesa Yaakov Billig, wanda ya jagoranci haƙo abubuwa," amma babu shakka wannan na cikin abubuwan ban mamaki a wannan wuri, wanda za mu yi ƙoƙari gano amsa."
Farfesa Billig ya ce an ruguza ainihin ginin a lokacin mamayar Babylonian a Birnin Ƙudus a shekara ta 586 kafin haihuwar Annabi Isa.

Asalin hoton, Yaniv Berman/Israel Antiquities Authority
IAA ta ce duk wanda ya ga abin da aka gano dole ya ƙayatar da shi a yankin da aka fi sani da Birnin David ko Wadi Hilweh a harshen Larabci, da kuma wurin bautar Yahudawa da suke kira Temple Mount su kuma Musulmi ke kiransa da Haram al-Sharif.
Masu waɗannan abubuwa na iya zama daya daga cikin sarakunan Judah ko kuma iyalai masu arziki, a cewar IAA.
Silalla ɗauke da hatimi da aka haƙo, na kama da waɗanda aka yi amfani da su tun lokacin Daular Judah na Isra'ila, sannan sun yi kusan ɗaya da tsabar kuɗin Isra'ila na yanzu.











