Jirgi na farko ya tashi daga Isra'ila zuwa Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa

Asalin hoton, Reuters
A karon farko wani jirgin fasinja zai tashi daga Isra'ila zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa a safiyar yau Litinin bayan da kasashen biyu suka amince su sabunta dangantaka.
A cikin jirgin akwai wata tawaga ta jami'an gwamnatin Ista;ila da na gwamnatin Amurka da suka taimaka aka kulla yarjejeniyar - wadda ita ce irinta ta uku da Isra'ila ta kulla da wata kasar Larabawa.
An rubuta kalmar "salama" boro-boro a gefen jirgin sama na El Al da bakake cikin Larabci da Ingilishi da kuma Hebrew.
Jami'an Isra'ila da ke cikin jirgin za su tattauna da takwarorinsu na HDL domin kulla yarjeniyoyi ta suka hada da bude ofisoshin jakadanci da zirga-zirgar jama'a tsakanin kasashen da kuma kasuwanci.
Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce jami'an kasar sun tattauna a cikin sirri da wasu kasashen Larabawa masu dama da zummar inganta dangantaka da kasarsa.
Benjamin Netanyahu:
"Idan sai mun jira Falasdinawa kafin mu zauna lafiya, to har abada za mu yi ta jira. Amma komai ya sauya. Abubuwa biyu ne suka sauya komai: Na farko shi ne shirin Mista Trump, na biyu kuma hadin kan kasashen Larabawa, wadanda Amurka ta taka gagarumar rawa domin ciyar da shirin zaman lafiyar ba tare da Falasdinawa sun kawo cikas ba."
Mai bai wa shugaban Amurka shawara kan batutuwan tsaro, Robert O'Brien tare da Jared Kushner wanda surukin shugaba Trump ne kuma mai ba shi shawara kan siyasar Gabas ta Tsakiya sun gana da mista Netanyahu ranar Lahadi.
Za su shiga tawagar jami'an Isra'ila da za su ziyarci HDL a karon farko cikin wani jirgin fasinja da zai isa can a yau Litinin.
Mista Kushner ya yaba wa kokarin da kasashen biyu suka yi da ya haifar da sabunta dangantaka tsakanin kasashen biyu:
"Za mu ci gaba da bibiyar hanyoyin wanzar da zaman lafiya tsakanin Isra'ila - wadda ita ce kasar Yahudawa cikin littafin Babul - da makwabtanta Larabawa da Musulmi, kuma ina da karfin gwuiwa hakan zai samu."
Mista O'Brien ma ya ce akwai kasashen Larabawa da na Musulmi da za su bi sahun HDL wajen kulla dangantakar kasuwanci da na diflomasiyya a watanni masu zuwa.
Sai dai Falasdinawa sun yin tir da matakin HDL wanda dukkan kasashen Larabawa suka dade da yanke shawara ba za su kulla dangantaka da Isra'ilar ba sai an warware matsalar Falasdinawa da Yahudawa baki dayanta.











