Isra'ila da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa sun cimma yarjejeniyar zaman lafiya

Composite image of Benjamin Netanyahu and Abu Dhabi Crown Prince Mohammed bin Zayed Al Nahyan

Asalin hoton, Reuters/Getty Images

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa ƙasashen Israila da Haɗaɗdiyar Daular Larabawa sun cimma yarjejeniya domin yin ƙawance irin na Diflomasiyya

A wata sanarwar haɗin gwiwa da Mista Trump da Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da Yarima mai jiran gado Mohammed Al Mahyan suka fitar, sun bayyana cewa "wannan mataki na ci gaba mai ciki da tarihi da aka samu zai kawo zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya".

Sun kuma bayyana cewa hakan na nufin Isra'ila za ta dakatar da yunƙurin da take yi na mamaye wani yanki na Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.

Har yanzu dai, Isra'ila ba ta da wata alaƙa ta diflomasiyya da ƙasashen Larabawa da ke yankin Gulf.

Wannan yarjejeniyar da aka cimma ita ce ta uku tsakanin Isra'ila da ƙasashen Larabawa tun bayan samun 'yancin kai na Isra'ila a 1948.

Masar ta sa hannu a yarjejeniya ta farko a 1979 sai kuma Jordan ta sa hannu a ta biyu a 1994.

A makonni masu zuwa, tawagogi daga Isra'ila da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa za su hadu domin su tattauna kan zuba jari da yawon buɗe ido.

Ana sa ran kuma tattauna batun tashin jirage tsakanin ƙasashen da tsaro da sadarwa da batun kimiyya da al'adu da muhalli da dai sauransu.

Ƙasashen kuma za su shiga shirin Amurka na ƙaddamar da Manufofin Gabas Ta Tsakiya.