'Yan Israila na da 'yancin samun kasarsu - Yerima Salman

Asalin hoton, Getty Images
Yarima mai jiran gadon Saudiyya Mohammed bin Salman ya amince cewa 'yan Israila na da 'yancin samun kasarsu.
A wani lamari da ya nuna sauyin matsayin Saudiyyar, Yerima Mohammed ya shaida wa mujallar Atlantic ta Amurka cewa 'yan Israila da Palasdinawa kowane na da 'yanci akan kasarsu.
A hukumance dai Saudiyya ba ta amince da kasar Israila ba, sai dai an dan samu kyautatuwar dangantaka ta bayan fage tsakanin kasashen biyu.
Kasashen biyu dai na kallon Iran a matsayin babbar barazana gare ta, baya ga mayakan kungiyoyi masu tada kayar baya.
A yanzu ana samun sauye-sauye a kasar Saudiya inda a baya kasar mai ra'ayin rikau ba ta cika tsoma baki ba cikin wasu harkokin yankin gabas ta tsakiya.







