Saudiyya: Yadda wata mota ta kunna kai cikin Masallacin Ka'aba a guje

Saudiyya

Asalin hoton, Others

Bayanan hoto, Motar ba ta ƙarasa cikin masallacin ba sakamakon ƙanƙantar ƙofar
Lokacin karatu: Minti 1

Wata mota ta kutsa kai cikin Masallacin Ka'aba a guje, inda ta dangane da ƙofar shiga cikin masallacin ta 89.

Kamfanin dillancin labarai na Saudiyya, SPA, ya ruwaito mai magana da yawun gwamnan Makka, Sultan al-Dosari, na cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:30 na daren Juma'a.

Motar ta kunna kai ta Farfajiyar Sarki Fahd, wadda aka haɗe ta da masallacin daga baya.

Wani bidiyo da aka yaɗa a shafukan zumunta ya nuna yadda motar ta yi awon gaba da shingen kariya sannan ta dangane da ƙofar shiga masallacin.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Majiyoyi da dama sun shaida cewa motar ta shiga farfajiyar masallacin ne ta kan Titi na 15, wadda ita ce babbar hanyar da ta dangane da cikin Farfajiyar Sarki Fahd da ke Masallacin Harami.

Sai dai hukumomi sun bayyana cewa babu wanda ya jikkata a hatsarin sannan kuma an kama direban nan take. Wasu hotuna sun nuna yadda aka ɗaure hannayensa kafin a fita da shi.

"Motar ta dangane da ƙofar ne yayin da take mugun gudu a kan ɗaya daga cikin titunan da ke kusa da farfajiyar masallacin ta ɓangaren kudu. Babu wanda ya jikkata," in ji Sultan al-Dosari.

Ya ƙara da cewa: "An kama direban. Ɗan Saudiyya ne kuma ba ya cikin hankalinsa. An miƙa shi wurin masu shigar da ƙara."

Shingen da ake sakawa a bakin ƙofar masallacin ba masu ƙwari ba ne, abin da ya sa motar ta yi fatali da su, kamar yadda ake iya gani a bidiyon.

Shafin Haramain Sharifain ya ce nisan da ke tsakanin ƙofar da motar ta shiga zuwa cikin masallacin bai fi mita 230 ba.