Aikin Umrah: Sabbin sharuɗan da Saudiyya ta gindaya wa masu gudanar da ibadar

..

Asalin hoton, Getty Images

Mahukunta a Saudiyya suna sanar cewa za a kyale mazauna ƙasar su gudanar da ayyukan ibada na Umrah bayan ta dakatar da ita na tsawon watanni.

Hukumomin ƙasar sun ce daga baya za su kyale maniyyata daga ƙasashen waje su shiga ƙasar domin gudanar da ibadar wadda take da muhimmanci ga Musulmin duniya, sai dai za ta ƙayyade yawan maniyyatan da yawan ƙasashen da za ta bari su shiga ƙasar.

Maniyatta da ke cikin Saudiyya na iya yin Umrah daga ranar 4 ga watan Oktoba, inda maniyattan da ke ƙasashen ƙetare kuwa sai sun jira zuwa ranar 1 ga watan Nuwamba kafin su sami izinin shiga ƙasar.

Ma'aikatar Aikin Hajji ta Saudiyya ta kuma bayyana cewa idan annobar korona ta gushe, za ta kyale dubban maniyatta daga ko'ina a duniya su ci gaba da ziyartar biranen Makkah da Madin domin gudanar da ibadunsu.

Musulmi na iya yin ibadar Umrah a duk lokacin da suka so, ba kamar aikin Hajji ba da ake iya yi sau ɗaya kawai a kowace shekara.

Miliyoyin Musulmi daga sassan duniya kan tafi Saudiyya a kowace shekara domin sauke wannan muhimmiyar ibada da ke ta biyu ga aikin na Hajji a daraja.

Tun dai a watan Yulin bana hukumomin Saudiyya suka ɗauki matakai domin daƙile bazuwar annobar korona, A bana mutum 10,00 ne kawai suka yi aikin Hajji a maimakon kimanin miliyan biyu.

Yadda sharuɗan komawa Aikin Umrah suke

  • A karon farko dai kamar yadda ƙasar ta Saudiyya ta bayyana, za a bar kashi 30 cikin 100 na adadin waɗanda masallacin ya saba ɗauka su yi aikin Umrah a kullum, za a fara bari su yi aikin daga 4 ga watan Oktoba. Sai dai kuma 'yan ƙasar Saudiyya da baƙi mazauna ƙasar ne za a bari su rika gudanar da Umrar a karon farko, a lissafi kenan kusan mutum 6,000 za a bari a kullum bisa tsarin da masana lafiya suka bayar kan buɗe babban masallacin.
  • A tsari na biyu da aka fitar na dawo da aikin na Umrah, za a bar 'yan ƙasar da baƙi mazauna ƙasar su fara kai ziyara Rawdah a Madina da ke cikin Masallacin Manzon Allah (SAW). Za a bar kashi 75 cikin 100 na waɗanda aka saba bari su yi aikin a baya, wanda hakan ke nufin kusan maniyyata 15,000 a rana da kuma mutum 40,000 masu zuwa Sallah a Masallacin Makkah, da kuma kashi 75 cikin 100 da za su rinƙa zuwa Masallacin Madina.
  • A karo na uku, za a bar maniyyata daga ƙasashen waje shiga Saudiyya domin gudanar da Umrah daga 1 ga watan Nuwamba, inda ake sa ran masallatan za su koma ɗibar mutane masu yawa.