An tayar da bam a wata maƙabarta a Saudiyya

Asalin hoton, AFP
Mutane da dama sun jikkata a wani harin bam da aka kai wajen da jami'an diflomasiyya na ƙasashen waje suka taru don Ranar Tunawa da mutanen da suka mutu a Yaƙin Duniya na Ɗaya, a birnin Jiddah da ke Saudiyya, kamar yadda Faransa ta sanar.
Ofisoshin jakadancin Faransa da Girka da Italya da Birtaniya da Amurka sun ce wani bam ne ya tashi a wata maƙabartar da ba ta Musulmai ba a ranar Laraba da safe.
Wata sanarwar haɗin gwiwa da ƙasashen suka fitar ta yi Allah-wadai da harin inda suka ce 'hari ne da matsorata suka kai da bai dace ba".
Hukumomin Saudiyya sun tabbatar da cewa wani ma'aikacin ofishin jakadancin Girka da wani jami'in tsaron Saudiyya sun ji rauni.
BBC ta fahimci cewa wani ɗan Birtaniya ma ya ji rauni kaɗan.
Gwamnatin yankin Makkah ta bayyana harin a matsayin ''wanda matsaorata suka kai'' tana mai cewa tuni dakarun tsaro suka ƙaddamar da bincike.
A ranar 29 ga Oktoba ne, wani ɗan Saudiyya ya daɓa wa wani mai gadi a ofishin jakadancin Faransa wuƙa tare da ji masa rauni, kuma a wannan ranar ce aka kashe wasu mutum uku da wuƙa a birnin Nice na Faransa, laifin da aka zargi ''masu tsattsauran kishin Islama da yi.''
Wata ƴar jarida mazauniyar Saudiyya Clarence Rodriguez, ta wallafa hotuna a Tuwita da ke nuna yadda yanayin ya kasance bayan harin da aka kai na ranar Larabar, da suka haɗa da wani da ke nuna wani yadda ake bai wa wani da ya ji rauni agaji.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

"An kai wani hari maƙabartar da ba ta Musulmai ba da safiyar yau a Jiddah.
"An raunata mutum...[13] kwanaki kaɗan bayan harin wuƙa da aka kai a ofishin jakanci, an sake kai wa Faransa hari?"
Ta ƙara da cewa wani jami'in tsaro dɗn ƙasar Girka wanda bai saka kayan sarki ba ya ji rauni matuƙa. Ta ce tuni aka kai shi ofishin jakadancin Girka.
Wani jami'in jakadancin Girka ya bayyana wa Reuters cewa mutum huɗu sun samu rauni a yayin harin, ɗaya daga ciki kuma ɗan asalin ƙasar Girka ne.
Ma'ikatar harkokin waje ta Saudiyya ta yi kira ga gwamnatin ƙasar da "ta yi ƙarin haske kan wannan harin, tare da ganowa da kuma ɗaukar mataki kan waɗanda suka kai harin".











