Senegal: Ana fargabar yan cirani 100 sun nutse a teku

A ƙalla ƴan cirani 100 ne su ka ɓata a gabar tekun Senegal kilomita 80 kafin su isa Ganga.
Lamarin ya faru ne bayan da kwale-kwalen da su ke ciki ya kama da wuta ya kuma nutse.
Rahotanni sun ce suna kan hanyar su ce ta isa tsibirin Canary da ke Sfaniya, a lokacin da ɗaya daga cikin injinan jirgin ya samu matsala.
Kuma a daidai lokacin da ma'aikatan jirgin ke kokarin gyara shi ne ya yi bindinga.
To sai dai rundunar sojin ruwan Senegal ta yi nasarar kuɓutar da mutum 59 daga cikin ƴan ciranin.
Hukumomi a Sfaniya sun kara tsaurara tsaro a yankin na Canary Island, lura da yadda yan cirani ke tururuwa yankin a kokarin su na ketarawa Tarayyar Turai.
Sama da yan cirani 1,000 ne su ka isa Canaty Islands a makonni biyun da su ka gabata, kamar yadda alkaluman kungiyar agaji ta Red Cross su ka nuna.
Kuma shi ne adadi mafi yawa tun bayan shekarar 2006, a lokacin da ƴan cirani 35,000 su ka isa yankin archipelago.











