An kama mutanen da ake zargi da ƙona ɗan Najeriya a Libya

Ma'aikatar harkokin cikin gida ce ta fitar da sanarwar kama mutanen.

Asalin hoton, TWITTER/KWESI QUARTEY

Hukumomi a Tripoli sun kama wasu mutane uku yan Libya da a ke zargi da kona wani dan Najeriya.

Ma'aikatar harkokin cikin gida ce ta fitar da sanarwar kama mutanen.

Sanarwar ta ce 'wasu matasa uku sun kutsa kai cikin wata ma'aikata a Tripoli inda yan cirani daga kasashen Afrika ke aiki, su ka kama daya daga cikin su, wanda dan Najeriya ne, su ka kuma yi masa wanka da man fetur su ka cinna masa wuta'.

To amma sanarwar ba ta yi karin haske game da dalilin da ya sa matasan su ka aikata danyen aiki.

Wakilin na musamman na hukumar kula da yan cirani ta duniya ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa 'ya kadu da abinda ya kira tsantsar ta'addanci da a ke nuna wa yan cirani a Libya'.

Dama yan cirani daga yan kin Afrika kudu da hamadar Sahara kan ya da zango a Libya, kafin su yi kokarin ketarawa kasashen Turai.