Ɗan Trump ya zubar da hawaye a taron jam'iyyar Republican

Babban taron jam'iyyar Republican na kasa a Amurka na ci gaba da kankama bayan shafe daren farko manyan jam'iyyar na gabatar da jawabai da nufin tallata dan takararsu na shugaban kasa Donald Trump.

Bakin masu jawabi a taron ya zo daya, kan cewa Donald Trump ne ya fi da cewa ya ci gaba da shugabancin kasar a halin da ake ciki, sannan Joe Biden da ke yiwa jam'iyyar Democrat takara bai cancanci yin jagoranci ba.

A jawabin da ta gabatar tsohuwar jakadiyar Amurka a majalisar dinkin duniya Nikki Haley, ta ce shugaba Trump ya farfado da kima da muhibbar Amurka a idon duniya

Ta kara da cewa shugaba Trump ya bada mamaki a shekaru hudu na mulkinsa, kuma babu wani shugaba da ya cimma nasarar da ya samu a shekaru hudu na farkon mulkinsa.

Sannan ta gargadi 'yan kasar da su kaucewa zabar jam'iyyar Democrat a zaben kasar na watan Nuwamba, in da tace zasu mayar da hannun agogo baya.

Dan shugaba Trump wato Donald Trump Jnr, na cikin wadanda suka yi jawabi kuma ya shaidi mahaifinsa da ya kira a matsayin mai kyakkyawan hali da ya kawowa kasar ci gaba.

Cikin kwalla, dan shugaban kasar ya ce ''Mahaifi na ya bautawa Amurka, kuma zai cigaba da bauta mata har karshen rayuwarsa''.

Sai dai ba a ji mahalarta taron sun yi wani jawabi na kyamar cin zarafin bakake da ake samu a kasar ba, duk da cewa ana gudanar da taron ne a dai-dai lokacin da masu zanga-zanga ke ci gaba da nuna fushinsu a kan titunan jihar Wisconsin, in da wani dan sanda ya budewa wani bakar fata wuta.

Tun da farko jam'iyyar ta Republican ta tsayar da Donald Trump da Mike Pence a matsayin dan takarar shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa a hukumance.

Sun yi alkawarin ci gaba da abin da suka kira ''Ciyar da Amurka gaba'', duk da halin da take ciki na annobar korona.

Za a kwashe tsawon kwana hudu ana gudanar da taron, in da a ranar karshe ake sa ran Donald Trump zai gabatarwa yan kasar jawabi a kan manufofin da yake son cimmawa a shekaru hudu da yake neman su bashi dama don ci gaba da shugabantarsu.