Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƴan Republican sun faɗa wa Trump: Ba ka da ikon jinkirta zaben 2020
Manyan ƴan jam'iyyar Republican mai mulkin Amurka sun yi watsi da kiran da Shugaba Trump yayi cewa a jinkirta zaben shugaban ƙasa da za a yi a watan Nuwamba mai zuwa saboda yana ganin za a tafka maguɗi.
Shugaban masu rinjaye a majalisar Dattawan ƙasar Mitch McConnell da Shugaban marasa rinjaye Kevin McCarthy duka sun yi watsi da shawarar.
Mista Trump ba shi da ikon dage zaben, domin tilas majalisa ta amince da duk wani jinkiri.
Tun da fari shugaban ya ce ƙaruwar masu aikawa da ƙuri'unsu ta gidan waya na iya sa wa a yi maguɗi.
Ya kuma ce a jinkirta zaben har zuwa lokacin da mutane za su iya yin zabe cikin yanayi na "natsuwa da tsari da tsaro". Babu wata shaida da ke nuna akwai matsala irin wadda Mista Trump ke bayyanawa.
Jihohin Amurka na son sauwwaƙa yadda ake aikawa da ƙuri'u saboda fargabar yaɗuwar cutar corona.
Matakin na MIsta Trump na zuwa ne a dai-dai lokacin da alƙaluma ke nuna tattalin arzikin ƙasar yayi ƙasa da kusan kashi 33 cikin 100 - matakin da ya bayyana girman lalacewar lamurra tun zamanin da aka fuskanci karyewar tattalin arzikin duniya na shekarun 1930.
Ya 'ƴan Republican suka karɓi shawarar?
Sanata McConnell ya ce ba a taba jinkirta zaben shugaban Amurka ba a tarihi.
"A tarihin ƙasarmu, ba a taba jingine zaɓukan tarayya ba, duk da matsaloli kamar yaƙi da koma bayan tattalin arziki da yaƙin basasa. Za mu samo hanyar yin haka a ranar uku ga watan Nuwamba mai zuwa," kamar yadda ya shaida wa tashar talabijin ta WNKY a Kentucky.
Mista McCarthy ma ya ɗauki irin wannan hanyar shi ma. "Ba a taɓa fasa yin zaben muƙaman gwamnatin tarayyarmu ba duk tsawon tarihin zaɓukan ƙasar nan kuma kamata yayi mu ci gaba mu yi zabenmu."
Wani na hannun damar MIsta Trump, Sanata Lindsay Graham ya ce jinkirta zaben "ba shawara ce mai kyau ba."
Amma sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya ƙi yarda ya ce wani abu game da shawarar ta Mista Trump. Da wasu ƴan jarida suka tambaye shi ko shugaban ƙasa na iya jinkirta zabe, sai ya ce ba zai "yanke hukunci kan batutuwa na shari'a ba cikin hanzari."
Kakakin ƙungiyar yaƙin neman zaben shugaban ƙasar, Hogan Gidley cewa yai Mista Trump na "tambayar ko ana iya yin haka ne kawai".
Me Trump ya ce ne?
Yayin wata ganawa da manema labarai a Fadar White House ranar Alhamis, Mista Trump ya musanta yana son a daga zaben, amma ya kafe cewa aikawa da kuri'u masu yawa ta gidan waya na iya bayar da kafar yin maguɗi.
"Ba na son jinkiri, Ina bukatar a yi zaɓen," a cewarsa. "Amma ba na son sai an yi jiran wata uku sannan a gano duka kuri'un ba su nan sannan zaɓen bai yi tasiri ba ke nan."
"Ba na son ganin zaɓen da aka yi maguɗi," mista Trump ya sanar da manema labaran. "Wannan zaben zai iya kasancewa wanda aka fi murɗewa idan haka ya faru."
Cikin wasu jerin saƙonnin Tiwita, Mista Trump ya soki tsarin aikawa da kuri'un ta gidan waya har yana gargaɗi- ba tare da wata hujja ba - cewa ƙasashen waje na iya yin kutse cikin zaɓen."