Donald Trump: Dole kamfanonin Amurka su yanke alaƙarsu da TikTok da WeChat

Shugaban Amurka ya sanya hannu kan wata tsattsaurar doka da ta mai da hankali kan TikTok da WeChat, wadanda su duka manyan manhajojin kasar China ne.

Cikin wannan doka, dole ne kamfanonin Amurka su dakatar da harkokin kasuwanci da kafanonin Chinan cikin kwanaki 45, in ji Mista Trump wand ya ce "muna kokarin kare tsaron kasarmu ne".

Wannan na daya daga cikin abubuwan da ke kara rura wutar rikici tsakanin Amurka da China kan karfin kere-kere da fasaharta a fadin duniya.

Wanann sanarwar na zuwa ne daidai lokacin da kamfanin kwamfuyuta na Microsoft ke tattauna yadda zai sayi kamfanin TikTok din reshen Amurka nan da 15 ga watan Satumba wanda shi ne wa'adin da Trump ya bayar.

Dokar kan manhajar da ake aika bidiyon da ba shi da tsayi TikTok - wanda kamfanin China na RyteDance ya mallaka - da kuma kan manhajar tura sako ta WeChat da kamfanin Tencent ya mallaka shi ne matakin baya-bayan nan na kara matsin lamba kan China da gwamnatin Trump ke kokarin ganin ta cimma.

Umarnin da Trump ya bayar ana masa kallon da yiyuwar ya kasance ya yi daidai da tsarin doka, in ji masu sharhi.

Me Trump ya ce?

A duka dokar, Mista Trump cewa ya yi "ya fahimci cewa akwai bukatar kara daukar matakai kan yadda ake tafiyar da harkokin kasar musamman ta bangaran yada labarai da kuma yadda ake watsa su cikin jama'a".

Ya kara da cewa: "Yaduwar manhajar wayoyin salula da kasar China ke kirkira na ci gaba da zama barazana ga harkokin tsaron kasa da manufofin mu na harkokin kasashen waje da tattalin arzikin kasar baki daya."

Dukka ya kafa hujja kan dokokin da wani bangare na kundin tsarin mulkin Amurka game da harkokin tsaro da tattalin arziki.

Menene TikTok?

Manhajar da ke ci gaba da yaduwa cikin gaggawa a Amurka na samun kimanin mutane miliyan 80 da ke amfani da ita a kasar ko wanne wata - ta kuma samu karbuwa nan da nan a wajen 'yan kasa da shekara 20.

Suna amfani da manhajar domin yaɗa bidiyon da bai fi sakan 15 da yawanci ya shafi wasa da leɓe lokacin da suke bin wakoki, da barkwanci da kuma wasu abubuwa masu kama da siddabaru.

Kowa zai iya ganin bidiyon da aka sa daga masu bin shafinka har baki. A tsarinsa ko wanne shafi mutane na da damar gani, duk da dai a wasu lokutan wasu na rufe shafukansu sai kawai ga mutanen da ke binsu.

Anan iya aika sako tsakanin mutum biyu kawai amma wannan ya takaita ne kawai ga "Abokai".

Rahotanni na cewa masu amfani da manhajar na kai wa miliyan 800 ko wanne wata a fadin duniya, inda kuma kasuwarsa ta fi karfi a Amurka da India.

Sai dai Trump ya fada a dokar cewa, tuni India ta rufe manhajar TikTok, da kuma wasu manhajojin kasar ta China.

Menene WeChat?

WeChat ya zama kamar ruwan dare a wajen masu amfani da shi da ke da alaka da China, in da aka rufe mafi yawan manhajojin kafafen sada zumunta irinsu Whatsapp da Facebook.

An fi yiwa WeChat kallon kafar sada zumunta, amma ta wuce haka a zahiri - domin akan iya biyan kudi ta ciki, da sauran wasu kanana-kanaan abubuwa, neman kwanan wata neman labarai bayan amfanin da ake da Manhajar wajen aika sako irin na sada zumunta.

Ana tsammanin shi ne mafi kyau a irin tsaransa, wadanda ake aiki da su a iOS da Android.

Masana na ganin yana cikin hanyoyin da China suke amfani da shi domin bibiyar abubuwan da ke faruwa a cikin al'umma - saboda akan bukaci masu amfani da shi wadanda ake zargin suna yada jita-jita da su yi rijista ta hanyar amon ko sautinsu.

Martani daga 'yan Najeriya

Masu amfani da TikToko a Najeriya sun bi sahun wasu kasashe wajen yin tsokaci kan matakin na Shugaba Trump.

Wasu na ganin ya kamata a kori manhajar daga Amurka tun da dai akai ta a Najeriya kamar yadda Sercanucarr yake cewa.