Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lassa ta kashe mutum 41 a Najeriya
Akalla mutum 41 ne suka mutu sakamakon cutar Lassa a sassan Najeriya tun farkon shiga shekarar nan ta 2020 a cewar gwamnatin kasar.
Ministan lafiya na kasar, Osagie Ehanire ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Abuja, babban birnin kasar.
Kazalika Cibiyar hana yaduwar cututtuka ta kasar ma CDC ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a shafinta na intanet.
Ministan wanda ya yi karin haske kan cutar ta Lassa da ke ci gaba da yaduwa a kasar ya bayyana cewa kimanin jami'an lafiya biyu na daga cikin mutum 41 da suka mutu.
Ehanire ya kuma ce akwai mutum 258 da suka kamu da cutar daga sassan jihohin kasar 19.
A cewar ministan lafiyar, ya kamata mutane su rika kula wajen tsaftace muhallinsu tare da killace abincinsu daga fadawa tarkon beraye.
Wani jami'i a hukumar ta CDC Dakta Abubakar Jafiya ya ce kawo yanzu, kananan hukumomi 56 ne a Najeriya wannan cuta ta bulla a cikinsu.
A cewarsa, "hanyoyin da muke bi muke gane cutar Lassa ya karu, amma idan aka duba yanayin mutuwar da ake samu ya sauko da kashi 7 cikin dari."
'A shekarar da ta gabata, wadanda suka kamu kamar kimanin sama da kashi 19%, a wannan shekarar kuma kimanin kashi 16 cikin dari na wadanda suka kamu ne suke mutuwa.", in ji Dakta Jafiya.
Ya kara da cewa yawan mace-mace saboda cutar ta Lassa a yanzu ya ragu daga kashi 20 cikin dari zuwa kusan kashi 15 cikin dari.
Dakta Jafiya ya kuma ce akwai maganin da ake bai wa wadanda suka kamu da cutar domin samun sauki sabanin tunanin da ake cewa cutar ba ta da magani.
Ya ce suna aiki tare da jihohi wadanda su ne suke jagorantar yaki da cutar ta Lassa a kasar domin dakile bazuwarta.
Jami'in ya bayyana cewa "Mun tura ma'aikatan lafiya zuwa jihohi da yawa domin kai musu magunguna da kuma kayan kariya ga su ma'aikatan lafiyar da za su kula da masu dauke da cutar."
Ya ce a shekarar 2019, an yi babban taro kan Lassa a karon farko a duniya a kokarin ganin an dakile yaduwar cutar.
Edo da Ebonyi da Ondo su ne jihohin da suka fi fama da cutar ta Lassa kuma haka ne ya sa aka bude wajen gwajin cutar a jihohin, a cewar dakta Jafiya.
Baya ga jihohin uku, an kuma bude irin wadannan wuraren gwaji a Abuja da kuma Legas.
Ya jaddada cewa ana gudanar da gwajin cutar a kyauta.
Ya kuma shawarci jama'a da su gaggauta kai duk mutumin da aka samu da alamun cutar zuwa asibiti saboda akwai yiwuwar mara lafiyar ya yada cutar idan har ba a dauki mataki ba.
Dakta Jafiya ya bayyana cewa an fi samun cutar lokacin rani daga Nuwamba zuwa Mayu.
"A wannan lokacin rani ana kona jeji, idan an kona jeji beraye suna guduwa daga jejin su shiga cikin al'umma. Mun san cewa beraye su ne suke yada wannan cuta." in ji Dakta Jafiya.
Ya ce rashin tsaftace muhalli na janyo beraye su nemi inda datti yake kuma "a garin haka su taba abinci".
Ya shawarci jama'a da su rika wanke hannu akai-akai sannan su rika killace abincinsu.