Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya bayar da shawara kan cutar Lassa

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu, ya yi kira ga jama'a da su kula da tsaftar muhallinsu sannan su sanar da ma'aikatan lafiya rahoton alamomin bullar cutar Lassa da aka samu farkon makon nan a jihar.

Sarki Sanusi ya yi wannan kira ne a fadarsa a ranar Alhamis, yayin da yake jawabi game da rahoton bullar cutar mai saurin kisa, a jihar Kanon da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Ya kuma ja hankalin mutane ga bukatar killace abinci da abin sha da kuma wanke hannu a ko da yaushe, a wani mataki na ganin an magance kamuwa da cutar.

"Ya zama wajibi mu yi kira ga jama'a da su tabbatar sun sanar da ma'aikatan lafiya rahoton alamomin bullar wannan cuta, kuma su guji amfani da duk wani magani ko wata hanya ta gargajiya domin magance wannan cuta," a cewar Sarki Sanusi.

Sarkin Kanon ya kuma yi addu'ar samun sauki ga mutanen da suka kamu da cutar da kuma addu'ar rahama ga wadanda suka mutu sakamakon kamuwa da cutar.

Tun bayan da Lassa ta bulla a Kano, akalla mutum 300 ne ake sa wa ido bayan da aka yi zargin sun kamu da cutar.

Mene ne Zazzabin Lassa?

Dakta Nasiru Sani Gwarzo, masani ne kan harkar lafiya, kuma a hirarsa da BBC ya ce cutar zazzabin Lassa wata kwayar cuta ce ta 'Virus', mai haddasa tsananin zazzabi mai bullar jini a jiki, wanda ake kira a Turance - 'viral heamorraghic fever'.

Ita wannan cuta tana zuwa wata sa'in da wasu alamomi da ba ayyanannu ba kamar mura da mashako da samun matsalar numfashi.

Asalin cutar ana samun ta ne daga wurin daga nau'in wasu beraye da ake kira 'multimammet rats' a Turance.

Ita wannan nau'in beran ana samunsu ne a dazuka ko wajen gari ko kuma a gonaki.

Tana da nonuwa a jere irin na kariya ba irin berayen gida ba. To amma idan suka kamu da cutar, suna yada wa berayen gida.

'Hanyoyin kamuwa da cutar Lassa'

Yayin da mutum ya shaki kurar fitsarin wannan beran ko bahayansu ko ya taba wani danshi da ke fita daga jikin, ko kuma mutum ya ci wannan bera, sai ya kamu da wannan cutar.

Hakazalika idan akwai bera ko berayen da ke dauke da wannan cuta a cikin dakin ajiya wato 'store' sai masu sharar wurin suka shaki kurar, suna iya kamuwa da wannan cutar.

Tana shiga ta huhu da baki da makogwaro ko hanci. Haka kuma idan mutum ya kamu da cutar, wani ma ya zo ya taba shi, zai iya kamuwa shi ma da cutar.

Ana daukar cutar ne ta hanyar shakar iska mai dauke da cutar ko taba gumin jikin mutum ko fitsarinsa ko jininsa da dai wani danshi da zai fito a jikin mai dauke da ita.

Ba a cika ganin alamominsu da wuri ba, har sai cutar ta yi barna.

Ma'aikatan jinya ko na kiwon lafiya sun fi shiga hadarin kamuwa da wannan cuta saboda mu'amala da masu shi.

Latsa alamar lasifikar da ke kasa don sauraron hirar BBC Hausa da Dakta Nasiru Sani Gwarzo:

'Illolin cutar Lassa ga jikin dan adam'

Cutar Lassa na da illoli da daman gaske ga jikin dan adam. Duk wani wuri da ke da abinda ake kira a Turance 'Epithelial Lining' yana cutarwa.

Yana shiga kwakwalwa da koda da duk wani sashe na jikin dan adam. Illar cutar ya fi muni ga magudanan jini.

'Matakan kariya'

Idan mutum ya kamu da cutar Lassa, 'yan uwansa su yi hanzarin sanar da hukuma ta asibiti. Idan a gida yake, akwai dabarun da za a bi a dauke shi a kai shi asibiti ta hanyar da ba za a kamu da cutar ba.

Ana sa rigar kariya da safar hannu masu inganci kamar irin wadda ake amfani da ita idan mutum ya kamu da cutar 'ebola'.

Sai kuma a dora mai cutar a kan magani. Idan suka fara shan magani da wuri, sukan rayu su warke ba tare da cutar ta yi musu barna ba.

Danginsa su guji nacin cewa sai sun kai masa ziyara a asibiti, domin a nan ake dauko cutar.

Idan kuma an yi rashin sa'a ba a rayu ba rai ya yi halinsa, to nan ma, ka da danginsa suce sai dole an ba su gawar sun tafi da ita gida.

Domin kuwa ko ruwan wankar gawar kanta idan ta taba mutum, zai iya kamuwa da cutar Lassa.