Koriya ta Arewa na barazanar kai wa Japan hari

Asalin hoton, AFP
Koriya ta Arewa ta bayyana Firai Ministan Japan Shinzo Abe a matsayin ''sakarai'' wanda bai san siyasa ba kuma ta zarge shi da sukar gwajin makaman da ta yi a 'yan kwanakin nan.
Mista Abe dai ya soki Koriya ta Arewa bayan da kasar ta yi gwajin makamai masu cin dogon zango har sau biyu a ranar Alhamis.
Sai dai Koriyar ta hakikance kan cewa tana gwajin ''wani sabon kwanson harba makamai masu cin dogon zango.''
Tuni dama kwamitin tsaro karkashin Majalisar Dinkin Duniya ya dakatar da Koriya ta Arewa daga harba makamai masu cin dogon zango.
Kasar na fama da takunkumai da dama da suka shafi harba makamai masu linzami da kuma shirye-shiryen nukiliya.
Janye takunkumin na daya daga cikin burin da Koriyar ke son ta cimma a tattaunawarta da Amurka amma hakan bai yiwu ba tun bayan wani taro tsakanin Shugaban kasar Kim Jong-un da kuma Shugaba Donald Trump na Amurka inda aka kasa cimma matsaya.






