Koriya ta Arewa ta sake harba makamai

Asalin hoton, Reuters
Koriya ta Arewa ta yi gwajin harba wasu makamai masu linzami guda biyu, wadanda ba a gane sanfurinsu ba, zuwa cikin teku, kamar yadda hukumomin sojin koriya ta kudu suka bayyana.
Kasar ta harba makaman ne 'yan sa'o'i kadan bayan da ta ce a shirye take ta yi zaman tattaunawa kan batun kawar da makamanta na nukiliya da gwamnatin Amurka a karshen watan nan na Satumba.
Wannan shi ne wani kwakkwaran tayi na tattaunawa, tun bayan da ganawar Shugaba Trump da Kim Jong-un ta wargaje a Hanoi, babban birnin Vietnam a watan Fabrairu.

Asalin hoton, EUROPEAN PHOTOPRESS AGENCY
Hadakar shugabannin rundunonin sojin Koriya ta Kudu da ta bayar da wannan sanarwa ta ce, an harba makaman masu linzami ne na Koriya ta Arewa daga wata tasha a lardin kudancin Pyongan, suka tashi zuwa cikin teku inda suka fada a yankin gabar gabas.
A kan hakan ne Koriya ta Kudu ta shiga wani taron gaggawa na tsaro domin sanin matakin da ta za ta dauka kan lamarin ganin yadda makwabciyar tata take ta irin wadannan gwaje-gwaje.
A 'yan watannin dai gwamnatin Koriya ta Arewa ta yi gwajin sabbin samfuran makamai masu linzami da ke cin gajeren zango, a don haka idan har wannan gwajin na yanzu ya tabbata, gaskiya to zai kasance na goma kenan da Pyongan din ta yi daga watan Mayu zuwa yanzu.

Asalin hoton, AFP
Koriya ta Arewar ta kaddamar da wannan gwajin ne 'yan sa'o'i bayan da mataimakiyar ministanta na harkokin waje Choe Sun-hui ta fada a wata sanarwa cewa, gwamnatinsu a shirye take ta sake zaman tattaunawa da Amurka a wuraren karshen watan Satumbar nan.

Asalin hoton, Reuters
Ta ce taron zai iya kasancewa ne a lokaci da kuma wurin da bangarorin biyu suka amince.
Sai dai kuma Pyongyang din ta gargadi Washington cewa, akwai bukatar Amurkar ta zo da wata yarjejeniyar ta daban, ba kamar irin ta baya ba, idan ba haka ba tattaunawar za ta sake wargajewa.











