Karim Benzema ya ci wa Madrid kwallaye 172 a tarihi

Asalin hoton, Getty Images
Karim Benzema ya shiga jerin 'yan wasan Real Madrid da suka fi ci mata yawan kwallaye a tarihi, inda ya zura 172 a raga tun komawarsa can da murza-leda.
Benzema - dan kasar Faransa - yana mataki na takwas a jerin 'yan kwallon da suka fi ci wa Madrid kwallaye a tarihi, inda ya yi kan-kan-kan da Pirri wanda ya ci 172 a raga.
Dan wasan shi ne ya ci kwallo na biyu a wasan da Madrid ta doke Granada da ci 5-0 a gasar La Liga a ranar Asabar, hakan kuma ya zura 11 a raga a kakar bana.
Kwallayen da Benzema ya ci sun hada da guda 116 a gasar La Liga da 38 a gasar zakarun Turai da 14 a Copa del Rey da uku a kofin duniya na zakarun nahiyoyi da guda daya a super cup.
Benzema ya koma Real Madrid da taka-leda a shekarar 2009 daga Lyon.
Ga jerin 'yan wasa da yawan kwallayen da suka ci wa Madrid a tarihi:
- 1 Cristiano Ronaldo 381
- 2 Raúl 323
- 3 ArgentinaColombia 308
- 4 Carlos Santillana 290
- 5 Ferenc Puskás 242
- 6 Hugo Sánchez 208
- 7 Francisco Gento 182
- 8 Karim Benzema 172
- 8 Pirri 172
- 9 Emilio Butragueño 171







