BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
KAI TSAYE, Trump ya ce sojojin Amurka da na Najeriya sun kashe mataimakin shugaban IS na duniya
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Asabar 16/05/2026
Yadda aka sace ɗalibai a jihohin Borno da Oyo a Najeriya
'Yan bindigan sun sace ɗaliban da zuwa yanzu ba a tantance yawansu ba a wasu makarantu a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya da kuma jihar Oyo da ke kudu maso yammacin kasar a ranar Juma'a.
Newcastle ta dage kan farashin Gordon, Liverpool na son Diomande
Newcastle ta dage kan farashin da ta sanya wa Anthony Gordon, yayin da Liverpool ke duba yiwuwar ɗauko yan wasa 4, inda shi kuwa ɗan wasan Brentford Michael Kayode, ya ƙi amincewa da tayin Juventus.
Bambancin yadda ƴan Arewa da ƴan Kudu ke zaɓe a Najeriya
A siyasar Najeriya, ɓangaren da dan takara ya fito da kuma addini na taka rawa sosai wajen zaɓe, sai dai babu wani abu ɗaya tilo da za a ce shi ne al'ummar dukkanin ɓangarorin ƙasar za su dogara da shi wajen zaɓen shugaba.
Abin da ya kamata ku sani kan zaɓukan fitar da gwanin APC
A yau ne jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya za ta fara gudnar da zaɓukar fitar da gwani na waɗanda ke son tsaya mata takara a zaɓukan 2027 da ke tafe.
Me ya sa Iran ta fi kai hare-hare kan Daular Larabawa?
Ana za ayoyin tambayoyin ne bayan wani rahoto da shafin Axios na intanet, ya ce jami'an Amurka da na Isra'ila sun nuna cewa sojojin saman UAE na da hannu a hare-haren da aka kai wa Iran.
'Boko Haram ta sace ɗalibai a Borno'
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Juma'a 15/05/2026
Ƙasashe bakwai da suka fi fama da ƙarancin ruwan sama a duniya
Masana sun ce yawancin ƙasashen da ke fama da irin wannan yanayi na ƙarancin ruwan sama suna a yankuna ne na rairayin hamada, kamar Sahara a Afirka da kuma yankunan rairayi na Gabas ta Tsakiya.
Mece ce gaskiyar shekarun Mahmud Buba da aka fi sani da Abin Al'ajabi?
A hirar matashin da ya yi da BBC a makon da ya gabata, Mahmud Buba ya bayyana wa kafar cewa shekarunsa sun haura 25 wanda hakan zai ba shi damar tsayawa takarar kujerar majalisar wakilai bisa doka.
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Yamma, 19:29, 16 Mayu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Hantsi, 06:30, 16 Mayu 2026, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Safe, 05:29, 16 Mayu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Ra’ayi Riga, 19:29, 15 Mayu 2026, Tsawon lokaci 1,00,00
Shiri ne a duk ranar Juma'a da ke baiwa masu sauraro damar bayyana ra'ayoyinsu.
Wasanni
Beckham ya zama biloniya na farko daga Burtaniya a fannin wasanni
Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga 11 zuwa 16 ga watan Mayun 2026.
Manchester City da PSG na hamayya kan Valverde, Arsenal na zawarcin Fernandez
Manchester City da PSG na zawarcin ɗan wasan tsakiya na Real Madrid Federico Valverde, Arsenal ta ƙwallafa rai kan ɗan wasan West Ham Mateus Fernandes.
Ko Mourinho zai iya gyara Real Madrid?
Sabon babi ne ake fatan buɗewa na kawo muhimmin canji a Real Madrid, sanin cewa Jose Mourinho zai dawo ƙungiyar bayan shekara 13 da raba gari da ita.
Gordon ya amince da komawa Bayern, Greenwood zai ci gaba da zama a Marseille
Bayern Munich ta cimma yarjejeniya da Anthony Gordon, Mason Greenwood na sha'awar ci gaba da taka leda a Marseille.
Abin da ya kamata ku sani kan Gasar Kofin Duniya ta 2026
Za a yaye labulen gasar ranar 11 ga watan Yuni a filin wasa na Estadio Azteca da ke birnin Mexico City na ƙasar Mexico.
Tashar WhatsApp ta BBC Hausa
A wannan shafin za ku samu labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya da ɗumi-ɗuminsu domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Kashe ƙwarƙwatar ido
Kuna son tattalin datarku?
Shiga shafinmu na labarai maras hoto domin rage zuƙar data
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Wane ne ya fara gina Ka'aba?
Alƙaluma sun nuna cewa aƙalla a kowace shekara akwai mutum miliyan 13 zuwa 15 da ke ziyartar ɗakin a duk shekara da suka haɗa da fiye da miliyan 11 da ke halartar Umra da kuma miliyan 2 zuwa 3 da ke zuwa aikin Hajji a kowace shekara.
Jadawalin manyan jam'iyyun siyasar Najeriya na zaɓen fitar da gwani
Manyan jam'iyyu huɗu a Najeriya sun fitar da jadawalin da suke shirin bi wajen gudanar da zaɓen fitar da gwani kafin babban zaɓen 2027.
Ko me ya sa hankalin ƴan adawa tashi kan alƙawarin wa'adi ɗaya na Peter Obi?
Jam'iyyun hamayyar ƙasar sun yi watsi da kalaman nasa, inda suka bayyana su a matsayin na yaudara da neman jan hankalin jama'a.
Waɗanne ƙasashen Larabawa ne ke ɗasawa da Isra'ila?
Ƙasashen Larabawa da dama na bayyana rashin amincewa da Falasɗinu da mamayar Isra'ila a Gaza a matsayin dalilin rashin shiga diflomasiyya da Isra'ila.
Abin da zai iya hana ka auren mace fiye da ɗaya
Sheikh Ahmed el-Tayeb ya ce auren mace fiye da ɗaya abu ne da ya dogara kan wasu sharuɗɗa.
Ta yaya za a iya aiwatar da hukuncin ɗaurin shekara 75 kan Saleh Mamman?
Lauyan ya bayyana wa BBC cewa yanke wa mutum hukunci ba ya nan ko ba ya gaban kotu na nufin kotu ta ci gaba da shari'a tare da yanke hukunci alhali wanda ake tuhuma bai halarci zaman kotun ba.
Tsakanin Boko Haram da ƴanbindiga waɗanne suka fi haɗari ga Najeriya?
Yawanci maharan suna da alaƙa ne da ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi na al-Qaeda da IS sai kuma ƙungiyoyin ƴanbindiga.
Manyan ƙalubale da ke hana matasa yin takara a Najeriya
Wasu matasan na da buri da hangen nesa na kawo sauyi a al'ummarsu, amma suna ganin akwai manyan ƙalubale da ke hana su taka sahihin mataki zuwa siyasa
Tinubu ya gargaɗi masu siyasar a mutu ko a yi rai a zaɓen fitar da ƴantakara
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Alhamis 14//05/2026
Yadda maslahar tsayar da Shekarau ta bar baya da ƙura
Alamu sun nuna cewa maslahar da aka yi a jam'iyyar APC da ta kai ga tsayar da Malam Ibrahim Shekarau a matsayin ɗan takarar sanatan Kano ta tsakiya, ta bar baya da ƙura.
Yadda Iran ke amfani da ƙananan jiragen ruwa wajen gallaza wa Amurka a Mashigar Hormuz
Ƙananan jiragen ruwan na daga cikin dabarun yaƙin Iran wajen ƙalubalantar ƙasashe masu manyan makamai irin Amurka.
Ko shan lemun kwalba mai sa kuzari na da illa ga matasa?
A yau, shan lemun da ke sa kuzari da ake kira da energy drinks ya zama ruwan dare a birane da ƙauyuka da dama.
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.





























































