Kylian Mbappe bai fitar da ran yi wa Real Madrid tamaula ba

Kylian Mbappe

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kylian Mbappe zai ci gaba da taka leda a PSG zuwa karshen 2025

Dan kwallon tawagar Faransa, Kylian Mbappe ya ce har yanzu ya na da mafarkin buga wa Real Madrid tamaula a nan gaba.

A karshen mako ne dan wasan ya sajka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da yi wa Paris St Germain tamaula zuwa karshen kakar 2025.

Mai shekara 23 bai amince ya koma Real Madrid da taka leda ba, wanda tun farko ya amince da tayin da ta yi masa, daga baya ya zabi PSG.

A hirar da ya yi da wakilin BBC Sports, Guillem Balague ranar Litinin, Mbappe ya ce bai fitar da ran nan gaba zai taka leda a Real Madrid ba.

''Bakasan mai zai faru nan gaba ba, lokaci za a jira,'' in ji dan wasan.

Mbappe wanda ya lashe Ligue 1 a bana ya fara taka leda a Monaco daga nan ya koma PSG a 2017 a matakin aro daga baya ta mallaki dan kwallon.

Tun bayan da Mbappe ya koma PSG ya lashe Ligue 1 hudu da French Cup uku.