Liverpool 1-0 West Ham United: Liverpool na jiran Man City ta yi ɓari

Sadio Mane ya ci kwallo hudu a wasanni uku a jere Premier

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Sadio Mane ya ci kwallo hudu a wasanni uku a jere Premier

Liverpool ta datse yawan makin da ke tsakaninta da Manchester City zuwa maki uku bayan doke West Ham a Anfield.

Sadio Mane ne ya ci wa Liverpool ƙwallon a ragar West Ham wanda yanzu tazarar maki uku ne tsakanin Liverpool da Manchester City.

Sakamakon bai yi wa West Ham daɗi ba yayin da take shirin haɗuwa da Sevilla da Europa League.

Wannan babbar nasara ce ga Liverpool, yayin da za ta zuba ido ta ga yadda za ta kaya tsakanin Manchester City da za ta karɓi bakuncin Manchester United a Etihad a ranar Lahadi.

Liverpool za ta ci gaba da matsin lamba ga City, inda Guardiola dole ya nemi yin nasara a karawarsa da United.

West Ham sau 70 tana shan kashi a haɗuwa da Liverpool, kuma sau ɗaya ta taba yin nasara Anfield a haɗuwa 52 kuma David Moyes ya kasa samun nasara a wasanni 66 a wasannin da ya buga a gidanmanyan ƙungiyoyin Premier Liverpool da Chelsea da Arsenal daManchester United.