Afcon 2021: Golan Equatorial Guinea da ya rasa damar mallakar safar hannun Michael Jackson

Asalin hoton, Getty Images/Teodoro Obiang Mangue
- Marubuci, Daga Piers Edwards
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Africa in Cameroon
Golan Equatorial Guinea Jesus Owono ya sami wani tayi da ya zaburar da shi gabanin karawar da ƙasarsa ta yi da Senegal a wasan kusa da na daf da karshe a gasar cin kofi kasashen Afirka, tayin kuwa shi ne zai iya mallakar safar hanun mawaƙi Michael Jackson.
Owoni mai shekara 20 da haihuwa ya sami tayin mallakar safar ta Michael Jackson idan ya taimaki ƙungiyarsa cin kofin a wasan karshe da za a yi ranar Lahadi 6 ga watan Fabrairu.
Mataimakin shugaban kasar Teodoro Nguema Obiang Mangue, wanda wata kotun Faransa ta yanke wa hukuncin daurin shekara uku saboda samunsa da laifin cin hanci da rashawa a 2017 (hukuncin da aka jingine), shi ne ainihin mutumin da ya mallaki safar kuma ya yi wa gola Owono wannan tayin.
Kasar Equatorial Guinea ce ta 144 a jerin kasashe mafi kwarewa a fagen kwallon kafa a duniya, kuma a jiya ta kara da Senegal a wasan kusa da daf da na karshe, wasan da Senegal ta yi galaba.
Ta leko ta koma?
Da alama wannan rashin nasarar ta kawo ƙarshen damar da gola Owono ke da ita ta mallakar wannan safar hannun, wadda ke da darajoji akalla biyu:
- Ta farko ita ce alaƙarta da Michael Jackson ya sa tana da wata daraja ta musamman a tarihi, wanda ba ya misaltuwa ga masoyan mawakin
- Saboda wannan alakar, an taba sayen safar kan dala 330,000 ta Amurka a watan Disambar 2010.
"Sakamakon nasarorin da kungiyarmu ta Nzalang National ke samu a wannan gasar sun faranta mana rai matuka amma ina son mayar da hankali ne kan matashin golanmu Jesus Owono," in ji Obiang a wani sako na Twitter da ya wallafa.
Ya ce "Idan Equatorial Guinea ta lashe gasar cin kofin kasashen Afirka, zan yi masa kyautar wari daya na safar Michael Jackson saboda jaruntar da ya nuna yayin wannan gasar.
Owono na buga wasan kwallon kafa ne a kungiyar Deportivo Alaves ta kasar Sfaniya, kuma ya hana sauran kungiyoyi zura wa kungiyar Equatorial Guinea kwallo ko da daya a raga a gasar cin kofin kasashen Afirka da ake yi a Kamaru, kuma ya kasance kwararre wajen tare bugun daga kai sai mai tsaron gida.
Ya hana Kei Kamara zura kwallo a wasan karshe da kasarsa ta buga a zagayen da ka samar da kasashe 16 na gasar, wanda suka buga kungiyar kwallon kafa ta kasar Saliyo.
Ya kuma tare wasu bugun daga kai sai mai tsaron gida har guda biyu a karawar da Equatorial Guinea ta yi da kasar Mali wadda aka tashi 6 - 5.
Obiang shi ne dan Shugaba Teodoro Obiang Nguema Mbasogo na Equatorial Guinea, shugaba mafi tsawon mulki a nahiyar Afirka wanda ya kwace mulkin kasar a 1979, wanda kuma kungiyoyin kare hakkin bil Adama ke kiransa daya daga cikin shugabanni masu mulkin kama karya a Afirka.

Asalin hoton, Getty Images
Obiang dan shugaban kasa mai shekara 53 yayi fice kan facakar da yake yi da dukiya da kuma soyayyar da yake wa dukkan kayan da Michael Jackson ya taɓa mallaka.
An nada shi minista a gwamnatin kasar Equatorial Guinea a 1998.
Cikin fitattun abubuwan da ya mallaka akwai wannan safar hannu da aka kayata da duwatsun lu'u-lu'u wadda mawaki Michael Jackson ya sanya yayin wani bikin waka da ya zagaya kasashen duniya mai suna "Bad Tour" a shekarun 1980.
Akwai kuma wasu kayan sanyawa uku na mawakin da ke cikin kayan da ya mallaka.
Michael Jackson, wanda aka fi sani da sunan King of Pop (Sarkin Wakokin Zamani), ya lashe lambobin yabo na Grammy har 13, kuma kundin wakokin da ya fitar na Thriller shi ne kundin wakoki da ya fi kawo kudi a tarihi. A shekarar 2009 Michael Jackson ya mutu yana mai shekara 50 da haihuwa.
Ga koshi ga kwana da yunwa
Ba wannan ne karon farko da mataimakin shugaban kasa Obiang ya taɓa yi wa kungiyar kwallon kafa ta kasar irin wannan tayi mai tsoka ba.
A 2012, bayan da kasar ta dauki nayin gasar cin kofin kasashen Afirka tare da kasar Gabon, Obiang ya biya kungiyar kwallon kafa ta kasar dala miliyan 1 bayan da ta doke takwararta ta Libya a wasan farko da aka yi a gasar.
Equatorial Guinea karamar kasa ce a gabar tekun Afirka ta Yamma, wadda a 1995 ta gano albarkatun man fetur a cikin kasar kuma tana cikin kasashe manya masu fitar da man fetur a Afirka.
Sai dai duk da dumbin arzikin da kasar ta mallaka, yawancin al'ummar kasar miliyan 1.4 na rayuwa cikin talauci ne.

Asalin hoton, Getty Images
Karin bayanai daga Rob Stevens.











