Afcon 2021: Abin da ya kamata ku sani kan wasan Tunisia da Mali

Kofin Afirka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Za a bayar da dalar Amurka miliyan biyar ga duk kasar da ta dauki kofin na bana

Rukuni na shida zai fara wasa ranar Laraba, inda za a kara tsakanin Tunisia da Mali a gasar kofin Afirka da ake yi a Kamaru.

Wasan rukuni na shida:

Rana: 12 Janairu 2022

Lokaci: 14:00 agogon Kamaru (13:00 GMT)

Fili: Limbe Omnisports, Limbe

Rukuni na shida:

  • Laraba, 12 Janairu: Tunisia da Mali, Mauritania da Gambia
  • Lahadi, 16 Janairu: Gambia da Mali, Tunisia da Mauritania
  • Alhamis, 20 Janairu: Gambia da Tunisia, Mali da Mauritania

Tunisia da Mali

Wasa biyu a baya da suka kara Tunisia ba ta ji dadi ba a hannun Mali a gasar Afcon, inda Mali ta yi nasara da ci 2-0 a 1994 da yin 1-1 a 2019.

Wannan shine karo na 20 da Tunisia ke buga gasar Afirka kuma karo na 15 a jere tana halarta.

Ta kuma lashe kofin a 2004 lokacin da ta karbi bakuncin wasannin, tun daga nan sau daya ta kai Quarter finals a 2019.

Wannan shine karo na 12 da Mali ke halartar Afcon, Senegal ce kan gaba a yawan buga gasar kofin Afirka amma bata lashe kofin ba, sai kuma Mali ke biye da ita.

Gasar da tafi yin kokari itace a 1972 da aka yi a Kamaru wadda ta yi rashin nasara a hannun Congo da ci 3-2 a wasan karshe.

Mali ba ta taba yin rashin nasara a wasan farko na cikin rukuni ba, wadda ta ci karawa shida da canjaras biyar.

Tun daga 2010 ba wata kasa da ta ci kwallo daga wajen da'ira ta 18 kamar Mali mai tara a raga daga 30 da ta ci a Afcon.

Farouk Ben Mustapha

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kyaftin din Tunisia, Farouk Ben Mustapha

Tunisia

Halarta: 20Kwazo: Lashe kofin a 2004

Koci: Mondher KebaierKyaftin: Wahbi Khazri

Matakin Fifa: 30Suna: Carthage Eagles

'Yan wasan Tunisia

Masu tsaron raga: Farouk Ben Mustapha (Esperance, Tunisia), Bechir Ben Said (US Monastir, Tunisia), Ayman Dahmen (Sfaxien, Tunisia), Ali Jemal (Stade Tunisien, Tunisia).

Masu tsaron baya: Dylan Bronn (Metz, France), Montassar Talbi (Rubin Kazan, Russia), Bilel Ifa (Club Africain, Tunisia), Oussama Haddadi (Malatyaspor, Turkey), Omar Rekik (Arsenal, England), Mohamed Drager (Nottingham Forest, England), Mohamed Amine Ben Hamida (Esperance, Tunisia), Hamza Mathlouthi (Zamalek, Egypt), Ali Maaloul (Al-Ahly, Egypt), Ali Abdi (Caen, France).

Masu buga tsakiya: Mohamed Ali Ben Romdhane (Esperance, Tunisia), Aissa Laidouni (Ferencvaros, Hungary), Ellyes Skhiri (Cologne, Germany), Ghailene Chaalali (Esperance, Tunisia), Seif-Eddine Khaoui (Clermont, France), Anis Ben Slimane (Brondby, Denmark). Hannibal Mejbri (Manchester United, England), Firas Ben Larbi (Ajman, UAE), Wahbi Khazri (Saint Etienne, France), Hamza Rafia (Standard Liege, Belgium), Naim Sliti (Al-Ittifaq, Saudi Arabia).

Masu cin kwallo: Seifeddine Jaziri (Zamalek, Egypt), Yoann Touzghar (Troyes, France), Youssef Msakni (Al Arabi, Qatar).

Mali national team

Asalin hoton, Getty Images

Mali

Halarta: 12Kawzo: Ta biyu a 1972

Koci: Mohamed MagassoubaKyaftin: Hamari Traore

Matakin Fifa: 53Suna: The Eagles

'Yan wasan Mali

Masu tsaron raga: Djigui Diarra (Young Africans, Tanzania), Ismael Diawara (Malmo, Sweden), Ibrahima Mounkoro (TP Mazembe, DR Congo).

Masu tsaron baya: Senou Coulibaly (Dijon, France), Mamadou Fofana (Amiens, France), Massadio Haidara (Racing Lens, France), Boubacar Kiki Kouyate (Metz, France), Falaye Sacko (Vitoria Guimaraes, Portugal), Issiaka Samake (Horoya, Guinea), Moussa Sissako (Standard Liege, Belgium), Charles Traore (Nantes, France), Hamari Traore (Stade Rennes, France).

Masu buga tsakiya: Yves Bissouma (Brighton and Hove Albion, England), Mohamed Camara (RB Salzburg, Austria), Lassana Coulibaly (Salernitana, Italy), Aliou Dieng (Al Ahly, Egypt), Amadou Haidara (RB Leipzig, Germany), Romenigue Kouame (Troyes, France), Diadie Samassekou (Hoffenheim, Germany), Adama 'Noss' Traore (Hatayspor, Turkey), Hamidou Traore (Giresunspor, Turkey).

Masu cin kwallo: Kalifa Coulibaly (Nantes, France), Moussa Doumbia (Stade Reims, France), Moussa Djenepo (Southampton, France), Ibrahima Kone (Sarpsborg, Norway), Lassine Sinayoko (AJ Auxerre, France), Adama "Malouda" Traore (Sheriff Tiraspol, Moldova), El Bilal Toure (Stade Reims, France).