Rikicin kabilanci ya barke a yankin Arewa mai Nisa na Cameroon

Asalin hoton, Getty Images
Shaidu sun ce an kashe aƙalla mutum 12, wasu gommai kuma sun jikkata a rana ta biyu ta wani rikicin ƙabilanci tsakanin Shuwa Arab makiyaya, da kuma manoma 'yan ƙabilar Mosgoum a Kousseri, cikin lardin arewa mai nisa na Kamaru.
Rahotanni sun ce wasu manoma 'yan ƙabilar Mosgoum ne suka far wa garin Kousseri inda suka cinna wuta a kan kasuwar garin da gidajen wasu Shuwa Arab 'yan kasuwa.
Bayanai sun ce an ƙone ƙauyuka guda shida a karawar da aka yi ta baya-bayan nan jiya Laraba. Hukumomin Kamaru ba su fitar da wata sanarwa a bainar jama'a game da rikicin ba.
A cewar Shugaba Mahamat Idriss Deby na Chadi, 'yan Kamaru dubu 30 ne suka tsere zuwa Ndjamena sakamakon rikice-rikicen ƙabilanci. Ya dai yi kira ga al'ummar Chadi su nuna karimci ga 'yan gudun hijiran kuma ya yi kira ga ƙasashen duniya su shawo kan matsalolin ayyukan jin ƙai da aka shiga.
Rikicin a wannan karo ya faro ne ranar lahadi bayan taƙaddama kan mallakar filaye tsakanin Larabawa makiyaya da 'yan ƙabilar Mosgoum manoma yayin da sauyin yanayi ya ta'azzara ƙamfar ruwa. A cewar alƙaluman hukuma an kashe aƙalla mutum 26.
A shekaran jiya Talata, sai da Gwamna Bakari Midjinyawa ya je Logon Birni inda ya yi kira ga ɓangarorin biyu su kawo ƙarshen wannan faɗa kuma su zauna lafiya.
Ga alama dai ba a ji wannan kira nasa ba.
Gwamna Bakari dai ya kira wani taron tsaro a yau Alhamis da nufin lalubo hanyar magance rikici da kuma tallafa wa mutanen da rikici ya raba gidajensu da kuma waɗanda suka tsallaka iyaka zuwa gudun hijira.
A ranar 10 ga watan Agusta an kashe aƙalla mutum 32, kuma aka ƙona ƙauyuka guda 19 lokacin rikice-rikicen ƙabilanci a lardin arewa mai nisa na Kamaru, in ji Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya.











