Abin da ya sa ƴan awaren Kamaru da na Najeriya suka haɗe kai

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Armand Mouko Boudombo
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC
Rikicin ƴan aware na Kamaru na tsawon shekara biyar bisa ga dukkan alamu ya fara daukar wani sabon salo inda rahotanni ke cewa kungiyoyin awaren na bangaren da ke magana da Turancin Ingilishi na samun taimako daga kungiyar ƴan awaren Biafra ta makwabciya Najeriya.
Bayan hare-hare biyu da ƴan awaren na Kamaru suka kai inda suka hallaka sojojin Kamaru 15 a watan da ya gabata, hukumomin sojin sun fitar da wata sanarwa wadda a cikinta suka ce ƴan gwagwarmayar sun yi amfani da manyan makamai, abin da ya saba wa dokokin duniya.
A sanarwar hukumomin sun kara da cewa karin karfin da ƴan awaren ke samu na da alaka da hadin kan da suke samu daga wasu kungiyoyi na ta'addanci da ke aiki a wajen kasar.
Da aka tuntubi kakakin rundunonin tsaron Kamaru Kanar Cyrille Atonfack Nguemo, kan kungiyoyin da suka yi zargin na aiki tare da ƴan awaren, wadanda ke zargin bangaren kasar da masu magana da harshen Faransanci suka mamaye ya danne su, bai fada ba.
Takamaimai ba a san ko sojojin na Kamaru na zargin wata kungiya daya ba ce ko kuma suna da yawa masu taimaka wa ƴan awaren da kuma inda suke.
Amma kungiyar aware ta Kamaru, ta Ambazonia Defense Forces (ADF), ta tabbatar da yin hadaka da kungiyar aware ta Biafra ta ƴan kabilar Igbo da ke neman ballewa daga Najeriya, wadda ita ma take amfani da makamai, a yankin kudu maso gabshin Najeriya da ke da tazarar kilomita 150 (mil 90) kawai da iyakar Kamaru, ta bangaren da ke amfani da harshen Ingilishi.

Asalin hoton, AFP
Wani hoton bidiyo da aka sanya a shafin Facebook na kungiyar aware ta ƴan Ambazonia, ADF, a farko-farkon wannan shekara ya nuna jagoran majalisar ƴan Ambazonia, daya daga cikin kungiyoyin awaren na Kamaru biyu, Cho Ayaba, tare da jagoran kungiyar ƴan aware ta Biafra da ke Najeriya Nnamdi Kanu suna sanar da kulla alaka ta soji.
Dukkanin jagororin biyu sun bayyana cewa kungiyoyinsu za su yi aiki tare domin kare iyakarsu daya da tabbatar da musayar makamai da bayanan sirri da kuma mayaka.
Yaya girman wannan yarjejeniya yake?
Ra'ayin masu sharhi ya rabu. "Zuwa yanzu ba a san tasirin hadakar kungiyoyin ba," in ji Elvis Arrey, masani a kan harkokin Kamaru a kungiyar nazari da bincike ta International Crisis Group (ICG).
Sai dai shi kuwa, Raoul Sumo Tayo, masanin tarihi da harkar tsaro a yankin, ya ce bai kamata a rena wannan hadaka ba, domin za ta ba wa mayakan kungiyoyin biyu damar gudu su shiga yankunan juna ta yadda dakarun kasashensu ba za su iya kai wa ba.
Ya ce wannan zai ma fi tasiri a Kamaru, inda ya ce, kusan babu alamun sojojin kasar a yankin da ake fama da rikicin ƴan awaren, kafin a fara rikicin saboda haka ba su da wata cikakkiyar masaniya a kan yankin.
Gwamnatocin kasashen biyu a baya sun taba tattaunawa kan ba wa dakarun junansu ikon tsallakawa su shiga yankin juna musamman idan suna bin mayakan Boko Haram cikin arewaci amma babu wata yarjejeniya da aka cimma.
Daga ina manyan makaman ke fitowa?
Hukumomin Kamaru ba su bayar da wani cikakken bayani ba kan irin makaman da suka ce ana amfani da su illa, dan takaitaccen bayani na nuna makamai masu lalata igwa-igwa da bindigogin harba manyan makaman roka.
Wasu makaman ana samunsu ne daga hare-haren da ake kai wa kan dakaru da sauran jami'an tsaron kasar, in ji Mista Arrey na ICG.
Ya kara da cewa, "sauran makaman na zuwa ne daga Najeriya."
Shi kuwa Mista Tayo cewa ya yi, "Tun ma kafin rikicin na yankunan masu magana da Turancin Ingilishin, yankin Nekja Delta wuri ne da aka saba safarar makamai a yankin Afirka."

Hukumomin Najeriya galibi sukan kama makaman da ake kokarin safararsu zuwa yankin masu magana da Turancin Ingilishi na Kamaru.
A cikin shekara uku da ta gabata an kama mutane da yawa bisa laifin safarar makamai zuwa Kamaru.
Mista Tayo na ganin wasu makaman na iya fitowa daga wasu kasashen duniya da suke da yawan mutanen Kamaru masu amfani da harshen Ingilishi.
Daman a Amurka an tuhumi wasu ƴan yankin Ingilishi na Kamaru da zargin safarar makamai, ko da yake ba wanda kotu ta kama da laifi kawo yanzu.
Ita kuwa kungiyar aware ta ƴan Biafra daman ana zarginta da kai hare-hare kan ofisoshin ƴan sanda tana kwashe makamansu, makaman da a iya cewa za a iya tsallakawa da su iyaka ba.
Ya saukin tsallakawa iyaka da makaman yake?
Tun ma kafin wadannan tashe-tashen hankali na ƴan aware a kasashen biyu, babu wani kyakkyawan tsaro na iyakokinsu.
Yanki ne galibi daman da yake a bangaren Neja Delta, wanda surkukin daji ne mai tarin bishiyoyi da hanyoyi kanana da tashoshin boye na kananan kwale-kwale ko jiragen ruwa, da ke da iyaka da yankin masu magana da harshen Ingilishi na Kamaru da kuma yankin kabilar Igbo, inda yawanci ƴan IPOB suka fi kai hari.
Akwai alaka ta kabila da al'adu a tsakanin wasu mutane ko kabilun yankin a bangarorin kasashen biyu, wanda wannan ka iya tabbatar da mu'amulla a tsakaninsu.
Me hukumomin Kamaru ke yi a kai?
Kusan hukumomin Kamaru sun fi damuwa da lamarin, kuma tuni suka sanar da yin sauye-sauye a ayyukan sojojinsu a yankin, ba tare da bayar da wani cikakken bayani ba.

Asalin hoton, AFP
A karshen watan Agusta kasashen biyu suka cimma yarjejeniya ta kara tsaro a yankin iyakarsu mai tsawon kilomita dubu biyu (mil 1,240 ), yankin da ke fama da matsalar hare-haren ƴan aware da mayakan Boko Haram.
Haka kuma kasashen biyu sun hada kai a lokacin da aka kama jagoran ƴan aware na Kamaru Julius Sisiku Tabe da wasu mukarrabansa takwas a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya a 2017.
Daga nan aka mayar da su Kamaru, inda aka yanke musu hukuncin zaman gidan yari na rai da rai kan zargin ta'addanci da sauran laifuka, laifukan da suke kalubalanta.
A kan me ake rikici?
Dukkaninsu, ƴan kabilar Igbo da kuma ƴan Kamaru da ke yankin da ake amfani da harshen Ingilishi sun dade suna zargin gwamnatocin kasashensu da danne su.
Ƴan awaren kabilar Igbo sun ayyana ƴancin Biafra daga Najeriya a 1967, abin da ya janyo yakin basasa, wanda ya kare a 1970, bayan mutuwar akalla mutun miliyan daya.
Ko da yake dakarun gwamnatin Najeriya sun yi galaba, kungiyar IPOB ta Nnamdi Kanu ita ce ta baya-bayan nan da ta ci gaba da tawayen na ƴan kabilar ta Igbo.
An damke shi a watan Yuni, kuma a yanzu haka yana fuskantar shari' kan zargin laifukan cin amanar kasa, abin da ya musanta.
An kashe mutane da dama a tashe-tashen hankali da ke da nasaba da awaren tun daga shekarar da ta gabata.
Zanga-zangar da lauyoyi da malaman makaranta na yankin da ake magana da Turancin Ingilishi suka yi a 2016, kan dokokin da suke gani na fifita harshen Faransanci ta ta'azzara ta zama cikakken rikicin aware, inda wasu kungiyoyi suka ayyana ƴancin yankin da suka kira Ambazonia, a shekara ta 2017.
Bayan rahotannin da ake samu na gallazawa daga dukkanin bangarorin biyu, rikicin ya haddasa mutuwar dubban mutane tare da tilasta wasu dubbai tserewa zuwa cikin Najeriya.

Me ya sa aka samu masu magana da Ingilishi da Faransanci a Kamaru?
- A ranar 1 ga watan Janairu 1960, yankin Kamaru da ke karkashin Faransa ya samu ƴancin-kai inda ya zama Kamaru.
- A ranar 1 ga watan Oktoba 1960, Najeriya ta samu ƴancin-kai daga Birtaniya.
- Birtaniya ce kuma take iko da tsohon yankin Kamaru da ke karkashin Jamus. A lokacin bayar da ƴancin-kai, an bai wa ƴan yankin damar zaben kasar da suka fi so zu kasance karkashinta, tsakanin Najeriya da Kamaru.
- Ƴan kudancin Kamaru suka zabi hadewa da Kamaru, yayin da mutanen arewa suka zabi bin Najeriya












