Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Barcelona ta sake ɗaukar Dani Alves
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona ta cimma yarjejeniya da tsohon ɗan wasanta Dani Alves domin sake ɗaukarsa bayan shekara biyar da barinsa ƙungiyar.
Alves mai shekara 38 wanda ya lashe manyan gasa tara a Barca da Juventus da Paris St-Germain, zai koma kulob ɗin na Spain a kyauta don kammala wasannin gasar 2021-22.
Ɗan ƙasar Brazil ɗin ya shafe shekara takwas a Barca daga 2008 zuwa 2016, inda ya lashe La Liga shida da Zakarun Turai uku da kuma Copa del Rey huɗu.
Ƙungiyar ta siffanta shi da "ɗan wasan baya na gefen dama mafi ƙwarewa a tarihin Barca" cikin wata sanarwa a shafinta.
"Ɗan wasan zai isa Barca a mako mai zuwa amma ba zai iya buga wasa ba har sai watan Janairu," in ji sanarwar.
Tun farko Barca ta fasa ɗaukar Alves amma sabon mai horarwa Xavi ya nuna sha'awar dawo da shi tawagar domin taimaka mata dawowa kan ganiya.
A watan Satumba aka dakatar da kwantiraginsa a ƙungiyar Sao Paulo sakamakon rikici kan albashinsa.