Wasu kalubale takwas da ke gaban Xavi Hernandez a Barcelona

Ranar Talata Xavi Hernandez ya fara aiki a matakin sabon kociyan Barcelona, bayan da ya maye gurbin Ronald Koeman.

Tsohon dan wasan kungiyar ya koma Camp Nou daga Al Sadd ta Qatar, wadda ya lashe kofin babbar gasar kasar, kafin Barcelona ta bukace shi.

Bayan da aka gabatar da shi gaban magoya bayaranar Litinin ya fara jan ragamar atisaye ranar Talata, koda yake manyan 'yan wasan kungiyar sun je buga wa tawagoginsu wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya.

Hakan ne ya sa Xavi ya kira matasan karamar kungiyar don yin atisaye tare da suka hada da Mika Mármol da Álvaro Sanz da Ez Abde da Jutglà da Aranda da kuma Ilias Akhomach.

Xavi wanda ya amince da kunshin yarjejeniyar kaka uku, zai fara jan ragamar Barcelona wasan gasar La Liga ranar 20 ga watan Nuwamba da Espamyol a Camp Nou.

Sai dai kuma kocin zai fuskanci kaubale da yawa a lokacin da zai gudanar da aikinsa.

1. Ko Barcelona za ta kai zagaye na biyu a Champions League a bana?

Barcelona tana rukuni na biyar da maki shida, biye da Bayern Munich mai maki 12 a wasa hudu.

Benfica ta uku da maki hudu sai Dynamo Kiev mai maki daya bayan wasa hur hudu a cikin rukuni na biyar.

Ranar 23 ga watan Nuwamba Barcelona za ta karbi bakuncin Benfica, wadda ta ci kungiyar Sifaniya 3-0 a wasan da suka kara a Portugal.

Daga nan ne Barcelona za ta karkare karawar cikin rukuni da wasa a gidan Bayern Munich wadda tuni ta kai zagaye na biyu ta kuma doke Barca a Sifaniya da ci 3-0.

2. Ko Barcelon za ta lashe Champions League?

Rabonda Barcelona ta lashe Champions League tun kakar 2014/15, kuma karo na biyar a tarihi.

Xavi na bukatar hada 'yan kwallon da za su iya gogayya da kowacce kungiya a nahiyar Turai da ma duniya, domin ta ci gaba da taka rawar gani kamar yadda ta yi a baya.

3. Ko Barcelona za ta samu gurbin Champions League a badi?

Kawo yanzu Barcelona mai kwantan wasa, tana ta tara a teburin La Liga da maki 17, bayan cin wasa hudu a bana da canjaras biyar da rashin nasara uku.

Saboda haka wannan matakin ba zai bai wa kungiyar damar buga gasar Zakarun Turai ta badi ba kenan, koda yake da sauran wasanni da yawa da suka rage, amma ttana bukatar komawa cikin 'yan hudun farko.

4. Ko Barcelona za ta lashe La Liga?

Kofi na karshe da Barcelona ta dauka a La Liga shine a kakar 2018/19 kuma na 26 jumulla.

Daga nan ne Real Madrid ta dauka da kuma Atletico Madrid mai rike da kofin bara.

5. Ko Barca za ta dawo da martabarta a Camp Nou?

Kawo yanzuBarca ta yi wasa 16 a kakar bana a La Liga da Champions League da yin fafatawa tara a Camp Nou.

Bayern Munich ta ci Barcelona 3-0 a gasar Champions League a bana a gida da kuma Real Madrid da ta yi nasara a La Liga da ci 2-1 a Camp Nou da kuma canjaras da Getafe da kuma Alaves.

A baya duk kungiyar da za ta je gidan Barcelona tunaninta kada a zura mata kwallaye da yawa da kuma mamaye karawar da za su buga a tsakaninsu, sai dai yanzu an daina jin tsoron yin wasa a Camp Nou.

6. Ko Barcelona za ta dawo da salon taka leda ta bani in baka?

Barcecola ta yi suna wajen taka leda mai kayatarwa da duk kungiyar da ta kama kan ji a jikinta, sai dai yanzu ta sauya salon wasanninta an daina jin tsoron kungiyar kamar a baya.

7. Ko fitattun 'yan wasa za su amince su buga wa Barca tamaula?

Kungiyar Barcelona na fama da yawan 'yan wasa da ke jinya, hakan na nufin ya kamata kungiyar ta shiga kasuwa a cikin watan Janairun nan.

To sai dai Barcelona ta shiga matsin tattalin arziki da ta kai Lionel Messi ya bar kungiyar da Antoine Griezmann a kakar nan.

Messi ya koma taka leda a Paris St Germain, shi kuwa Griezmann ya koma buga wasannin aro a tsohuwar kungiyarsa Atletico Madrid.

Barcelona ta yi cefane kafin fara kakar bana da suka hada da Sergio Aguero daga Manchester City da kuma Memphis Depay daga Lyon, wadanda yarjejeniyarsa ya karkare a kungiyarsu.

'Yan wasan da ta sayo kuwa sun hada da Emerson daga Real Betis da Yusuf Demir daga Rapid Vienna da kuma Jordi Escobar daga Almeria.

8. Ko Barcelona za ta kare kofinta na Copa del Rey?

Kafin a kori Ronald Koeman ya lashe Copa del Rey a Sifaniya, saboda haja ko Xavi zai sake daukar kofin?