Xavi: Tsohon dan wasan Barcelona ya zama kocinta

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, ta naɗa tsohon dan wasanta, Xavi Hernandez, a matsayin sabon kocinta.

Ya gaji ɗan kasar Holland, Ronald Koeman, wanda aka kora a watan jiya.

Xavi ya lashe kofuna da dama a matsayinsa na dan wasa a Barcelona da Andulus, da suka hada da gasar cin kofin duniya da na Turai da gasar zakarun Turai da kuma La Liga takwas.

Tun da ya bar kungiyar ta Barcelona, Xavi ya kasance dan wasa kuma kocin kungiyar Al Sadd da ke Qatar, amma ana yawan danganta sunansa da kungiyar da yayi fice a cikinta.

A yanzu dai yanzu dai sabon kocin Barcelonar wato Xavi na son ganin cewa ɗan wasan Bayern Munich da Faransa Kingsley Coman mai shekara 25 ya zama ɗan wasa na farko da ya soma saya.