Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jerin wasannin da za su kara jefa Ole Gunnar Solskjaer cikin matsi
Wannan mako ba gasar Premier League, bayan da za a buga wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya.
A karshen mako aka kammala karawar sati na 11 a babbar gasar Ingila, inda Manchester United ta yi rashin nasara a hannun Manchester City da ci 2-0 a Old Trafford.
Hakan ne ya kai kungiyar mataki na shida a teburin Premier League da ta kai koci Ole Gunnar Solskjera ke fuskantar kalubale a kakar nan.
Tun kafin karawar ta sha kashi a gida da ci 5-0 a hannun Liverpool a gasar Premier League da rashin nasara a hannun Aston Villa da Leicester City.
United wadda aka fitar daga Carabao Cup a bana ta hada maki hudu a wasa shida baya, wadda ya kamata ta samu maki 18 a gasar Premier League.
Duk da fitar da kungiyar a Carabao Cup cikin watan Satumba, United tana ta daya a rukuni na shida da maki bakwai iri daya da na Villareal wadda take ta biyu.
Sai dai kuma Solskjaer zai iya kara tsintar kansa cikin matsi idan ya samu tangarda a wasu daga wasannin da ke gabansa da zarar an kammala wasanni neman gurbin shiga gasar kofin duniya.
Unitec za ta buga wasa mai zafi a gasar Premier League ranr 20 ga wwatan Nuwamba a gidan Watford.
Watford ba ta cikin 'yan kasan ukun teburi, amma tana taka rawar gani tun bayan da ta dauki Claudio Ranieri wanda yake da gogewa a gasar Premier League.
Daga nan ranar 23 ga watan Nuwamba United za ta buga Champions League a gidan Villareal, wadda United ta yi nasara a karawar da suka yi a Old Trafford da ci 2-1.
A fafatawar Villareal ce ta fara cin kwallo ta hannun Francisco Alcacer daga baya ta farke ta hannun Alex Telles, sannan Cristiano Ronaldo ya ci na biyu daf a tashi daga karawar.
Haka kuma a bara Villareal ta doke United a wasan karshe a bugun fenariti ta lashe Europa League.
United ce ta daya a rukuni na shida da maki bakwai iri daya da na Villareal a gasar ta Champion League.
Daga nan ne United za ta yi wasa na uku a waje ranar 28 ga watan Nuwamba, inda za ta ziyarci Chelsea a Stamford Bridge, wadda take ta daya a kan teburin Premier League.
Chelsea wadda ta yi wasa 11 ta ci karawa takwas da canjaras biyu da rashin nasara daya da cin kwallo 27 aka zura mata hudu a raga mai maki 26.
Ranar 2 ga wwatan Disamba United za ta karbi bakuncin Arsenal wadda take ta biyar a kan teburin Premier League, bayan da ta yi nasara a wasa uku a jere a gasar.
United za ta kara wasa na biyu a jere da karbar bakuncin Crystal Palace ranar 5 ga watan Disamba.
Palace dai tana kan ganiya tun bayan da Patrick Viera ya karbi jan ragamar kungiyar, wadda ta je ta ci Manchester City 2-0 a gasar Premier League a bana.
Wani wasa da ka iya zama kalubale ga Solskjaer shine wanda zai karbi bakuncin Young Boys ranar 8 ga watan Disamba a Champions League.
United dai ba ta kokari sosai a Old Trafford, kuma Young Boys ce ta fara cin United a karawar farko a cikin rukuni da ci 2-1 ranar 4 ga watan Satumba.