Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Solskjaer ya kafa tarihi a Manchester United
Sabon kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya kafa tarihi in da zama kocin kungiyar na biyu wanda ya lashe wasanninsa hudu na farko a kungiyar.
Wanda kawai ke a gabansa kuma na farko shi ne Sir Matt Busby dan asalin kasar Norway wanda ya fara kafa wannan tarihi a 1946.
A ranar Laraba ne 'yan wasan kungiyar suka buga wasan nasu da kungiyar Newcastle inda suka ci 2-0.
Lukaku da Rashford ne suka ci kwallaye dai-dai bayan an dawo hutun rabin lokaci.
Solskjaer ya yi nasarar cin wasannin nasa guda hudu inda kungiyarsa ta buga da Cardiff, Huddersfeild, Bournemouth da kuma Newcastle.
A ranar 19 ga watan Disamba ne aka tabbatar da Solskjaer- wanda tsohon dan wasan Man U ne a matsayin kocin kungiyar na rikon kwarya.
A yanzu Manchester United ce ta shidda akan teburin Premier inda take da maki 38, kuma take bi wa Arsenal wadda it ace ta biyar da maki 41.