Jose Mourinho: Manchester United ta kori Kocinta

Kungiyar Manchester United ta kori kocinta Jose Mourinho bayan ya shafe shekara biyu da rabi yana jagorantar kungiyar.

Mourinho mai shekara 55 ya lashe gasar League cup da kuma Europa League a zamansa na Manchester United.

A yanzu dai Manchester United ita ce ta shida a teburin gasar firimiyar Ingila,

inda Liverpool da ke matsayi na daya ta ba su tazarar maki 19, bayan a ranar Lahadin da ta gabata, United ta sha kashi a hannun Liverpool da ci 3-1.

Sanarwar da kulob din ya fitar ta ce za a nada sabon koci na rikon kwarya da zai jagoranci kungiyar har zuwa karshen kakar bana, yayin da za a fara laluben sabon koci da zai jagoranci kungiyar na din-din-din.

Sanarwar ta kuma ce "kungiyar ta gode wa Jose Mourinho saboda ayyukan da ya gudanar lokacin zamansa a kulob din, kuma tana yi masa fatan alheri."

Maki 26 da kungiyar ta hada bayan wasa goma 17 da ta buga a gasar wasannin Firimiya, shi ne mafi koma-baya da ta taba samu tun daga 1990.