Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jose Mourinho: Manchester United za ta farfado
Kocin Manchester United Jose Mourinho ya amince cewa babu dadi kungiya ta yi wasa biyar ba tare da samun nasara ba.
Kocin ya ci gaba da fuskantar matsin lamba bayan fuskantar babban kalubale a shekara 29.
Kungiyarsa ba ta ci wasa ko da guda daya ba tun bayan fara gasar firimiyar bana.
"Muna so mu kara azama. Muna bukatar maki don samun hakan - makin da muka rasa a wasanni biyun da suka wuce," in ji Mourinho.
Sai dai kocin ba ki ya yi karin haske kan abin da yake ganin ya jawo wannan rashin nasarar ga kungiyar yayin da yake ganawa da manema labarai a ranar Juma'a.
A ranar Asabar ne United za ta kara da kungiyar Newcastle United.
United ta buga kunnen doki (0-0) da Valencia a Gasar Zakarun Turai 'yan kwanaki bayan West Ham ta doke ta.