Solskjaer ya kafa tarihi a Manchester United

Man U ta lashe dukkanin wasannin ta hudu a karkashin Solskjaer

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto, Man U ta lashe dukkanin wasannin ta hudu a karkashin Solskjaer

Sabon kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya kafa tarihi in da zama kocin kungiyar na biyu wanda ya lashe wasanninsa hudu na farko a kungiyar.

Wanda kawai ke a gabansa kuma na farko shi ne Sir Matt Busby dan asalin kasar Norway wanda ya fara kafa wannan tarihi a 1946.

A ranar Laraba ne 'yan wasan kungiyar suka buga wasan nasu da kungiyar Newcastle inda suka ci 2-0.

Lukaku da Rashford ne suka ci kwallaye dai-dai bayan an dawo hutun rabin lokaci.

Rashford ya yi nasarar cin kwallon ta biyu da minti 80

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto, Rashford ya yi nasarar cin kwallon ta biyu da minti 80

Solskjaer ya yi nasarar cin wasannin nasa guda hudu inda kungiyarsa ta buga da Cardiff, Huddersfeild, Bournemouth da kuma Newcastle.

A ranar 19 ga watan Disamba ne aka tabbatar da Solskjaer- wanda tsohon dan wasan Man U ne a matsayin kocin kungiyar na rikon kwarya.

A yanzu Manchester United ce ta shidda akan teburin Premier inda take da maki 38, kuma take bi wa Arsenal wadda it ace ta biyar da maki 41.