Xavi: Wakilan Barcelona suna Qatar don kulla yarjejeniya da Al Sadd

Xavi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tsohon dan kwallon tawagar Sifaniya, Xavi ya fara horar Al Sadd tun daga kakar 2019

Al Sadd ta Qatari ba za ta bar Xavi ya motsa ba a wannan lokacin da yake da mahimmaci a kakar nan, duk da wakilan Barcelona sun je Qatar kan kulla yarjejeniya.

Tsohon dan wasan Barcelona, Xavi, mai shekara 41 shine ake sa ran zai maye gurbin Ronald Koeman da ta sallama.

A makon jiya Barcelona ta kori Koeman, kwana daya da kungiyar ta yi rashin nasara a hannun Real Madrid a El Clasico a gasar La Liga.

"Matsayin kungiyar a fayyace yake tun farko - za mu ci gaba da aiki da Xavi,'' in ji babban jami'in kungiyar Al Sadd, Turki Al-Ali.

"Ba za mu iya barin ya bar mu a wannan lokaci da yake da mahimmaci a kakar nan.''

Tun ranar Talata wakilan Barca da suka hada da Rafa Yuste da kuma Mateu Alemany suka isa Doha don tattauna wa da Xavi.

Barcelona tana mataki na tara a teburin La Liga, bayan da ta ci wasa daga 11 da fara babbar gasar tamaula ta Sifaniya da tazarar maki tara tsakaninta da Real Sociedad mai jan ragama.

Ranar Juma'a shugaban Barcelona, Joan Laporta ya ce ya tuntubi Xavi - wanda ya buga wasa 779 da lashe kofi 25 a Barca tsakanin 1998 zuwa 2015.