Manchester United: Ole Gunnar Solskjaer na son Jesse Lingard ya ci gaba da zama a kungiyar

Jesse Lingard

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jesse Lingard ya ci kwallo tara a wasannin da ya buga wa West Ham United aro a bara

Kocin Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer ya ce a shirye suke su ci gaba da rike Jesse Lingard, wanda kwantiraginsa zai kare a karshen kakar bana.

Mai shekara 28 dan kwallon tawagar Ingila ya taka rawar gani a wasannin aro a West Ham United, wanda ya ci kwallo tara a wasa 16 a bara.

Ya koma Old Trafford a bana aga West Ham, wanda ya ci kwallo na hudu a wasan da United ta doke Newcastle 4-1 ranar Asabar a Premier League.

Solskjaer ya ce ''Muna kallonsa a matakin fitatcen dan wasanmu na nan gaba.''

Dan wasan da ya fara daga karamar kungiyar United bai yadda da kunshin da kungiyar ta gabatar masa ba, hakan na nufin zai iya tattaunawa da wasu kungiyoyin cikin watan Janairu.

Solkjaer ya ce ''Jesse ya koma buga mana wasa bayan namijin kokarin da ya yi a West Ham, ya nuna kwarewar da yake da ita, Ingila na gayyatarsa wasanni, sannan yana cin kwallaye.''

Ranar Talata Young Boys ta doke Manchester United 2-1 a Switzerland, kuma Lingard ne ya yi kuskuren bayar da kwallo na biyu da aka ci United a wasan.

Ranar Lahadi 19 ga watan Satumba, United wadda take ta daya a kan teburin Premier League, za ta ziyarci West Ham United domin buga karawar mako na biyar.