Mikel Arteta na bakin ciki da Arsenal ba ta buga Europa League a bana

Mikel Arteta

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wannan shine karon farko da Arsenal ba ta buga gasar zakarun Turai tun bayan 1995

Mikel Arteta ya ce baya jin dadi da Arsenal ba ta cikin kungiyoyin da ke buga gasar Zakarun Turai ta Europa League ta bana.

Arsenal ta kare a mataki na takwas a kan teburin Premier League a bara, dalilin da ya sa ta kasa samun gubin shiga gasar Zakarun Turai ta bana a karon farko tun bayan 1995.

A kuma kakar 2021/22 hukumar kwallon kafa ta Turai ta kirkiro sabuwar gasa ta Europa Conference League, wadda Tottenham ke wakiltar Ingila, bayan da ta yi ta bakwai a Premier League da ta wuce a saman Gunners kenan.

Arteta ya ce zai yi amfani da wannan damar ta rashin buga gasar Turai domin taka rawar gani a kakar bana da lashe kofunan da za su faranta ran magoya bayan kungiyar.

Arsenal sai da ta yi kaka 20 a jere tana zuwa Champions League, amma ba ta dauki kofin ba tun Arsene Wenger, sannan ta koma buga Europa League.

Sai dai kuma Arsenal tana mataki na 16 a kasan teburin Premier League, wadda a makon jiya ta samu maki uku na farko a kakar nan, bayan doke Norwich City 1-0.

Gunners ta fara kakar bana da kafar hagu, inda aka zura mata kwallo tara a wasa uku ba tare da cin ko daya ba a Premier League.

Arsenal ta yi rashin nasara a gidan Brentford da ci 2-0 a wasan makon farko, sannan Chelsea ta doke ta 2-0 a Emirates da 5-0 da ta sha kashi a hannun Manchester City a Etihad.

Ranar Asabar 18 ga watan Satumba, Arsenal za ta jiyarci Burnley a wasan mako na biyar da fara babbar gasar Ingila.

Arteta zai ja ragamar Gunners ba tare da Granit Xhaka ba, wanda ke hutun dakatarwa wasa uku, bayan jan katin da aka yi masa a karawa da Manchster City a watan jiya.

Haka kuma mai tsaron baya, Rob Holding da mai taka leda daga tsakiya, Mohamed Elneny ba za su buga wasan ba, sakamakon jinya da suke yi.

Wasannin Premier League karawar mako na biyar:

Ranar Juma'a 17 ga watan Satumba

  • Newcastle United da Leeds United

Ranar Asabar 18 ga watan Satumba

  • Wolverhampton Wanderers da Brentford
  • Liverpool da Crystal Palace
  • Manchester City da Southampton
  • Norwich City da Watford
  • Burnley da Arsenal
  • Aston Villa da Everton

Ranar 19 ga watan Satumba

  • West Ham Unitedda Manchester United
  • Brighton & Hove Albion da Leicester City
  • Tottenham Hotspur da Chelsea