Romelu Lukaku: Dan wasan ya ci kwallo na 114 a Premier League a wasa da Arsenal

Asalin hoton, Getty Images
Chelsea ta je Gunners ta kuma yi nasara da ci 2-0 a wasan mako na biyu a gasar Premier League da suka fafata a Emirates ranar Lahadi.
Kungiyar ta Stamford Bridge ta ci kwallon farko ta hannun Romelu Lukaku a minti na 15 da fara wasa, sai Reece James ya kara na biyu saura minti 10 su je hutu.
Romelu ya ci kwallon sa na farko a fafatawa ta 16 a kaka tara da ya yi a Stamford Bridge, wadda ya fara buga mata tamaula cikin watan Agustan 2011.
Kuma kwallon da Lukaku ya zura a ragar Arsenal ya zama na 114 da ya ci a gasar Premier a West Brom da Everton da kuma Manchester United.
Wannan bajintar ya sha gaban Ian Wright, yana cikin 'yan wasa 20 da suka ci kwallaye da yawa a tarihin Premier League.
Haka kuma Lukaku ya zama na takwas a jerin wadanda ba 'yan kwallon Ingila ba da suka zura kwallo sama da 50 gida da waje a babbar gasar ta Ingila.
Shi kuwa Reece James ya zama na biyu a Chelsea da ya ci kwallo ya kuma bayar aka zura a raga a gidan Arsenal a Premier League, bayan Juan Mata cikin watan Satumbar 2012.
Lukaku mai shekara 28 ya koma Chelsea daga Inter Milan a makon jiya kan fam miliyan 97.5 a karo na biyu da zai buga mata tamaula, bayan zaman da ya yi tsakanin 2011 zuwa 2014.
Lukaku shine dan wasan da Chelsea ta saya mafi tsada a tarihi, kuma na biyu a tsada a Birtaniya, bayan Jack Grealish da Manchester City ta dauka daga Aston Villa a bana kan fam miliyan 100.
Dan wasan tawagar Belgium shine kan gaba a ci wa Inter kwallaye mai 24 a Serie A a kakar da ta wuce da kungiyar ta lashe kofin a karon farko tun bayan shekara 11.
Bayan da ya bar Stamford Bridge, Lukaku ya buga wasannin aro a West Brom da Everton daga nan kungiyar ta saye shi, ya koma Manchester United a 2017.











