Martin Odegaard: Dan kwallon Norway zai buga wa Arsenal League Cup raaanar Laraba

Sabon dan wasan da Arsenal ta dauka Martin Odegaard, zai buga wa kungiyar League Cup a wasa da West Bromwich ranar Laraba.

Tuni kuma Alexandre Lacazette ya koma atisaye a kungiyar, bayan da ya killace kansa, sakamakon kamuwa da cutar korona kamar yadda Arsenal ta sanar ranar Talata.

Arsenal tana ta biyun karshe wato ta 19 a kasan teburin Premier League, bayan shan kashi a wasa biyu a jere da ta buga da Brentford da kuma Chelsea a kakar bana.

Tuni kocin Arsenal, Mikel Arteta ya ce cutar korona ce ta kawo musu cikas, bayan da ta kama wasu fitattun 'yan wasan kungiyar daf da za a fara kakar bana, da wasu kuma ke jinya.

Sabon dan wasan da Arsenal ta dauka dan kwallon tawagar Norway mai shekara 22 daga Real Madrid, bai yi wa Arsenal karawar Premier League ba ranar Lahadi da Chelsea ta doke Gunners 2-0, sakamakon rashin takardar izinin shiga Birtaniya.

Lacazette yana cikin 'yan wasa hudu da ba su buga wa Arsenal wasan makon farko ba a Premier League a gidan Brentford, sakamakon kamuwa da cutar korona.

Sabon dan wasan da Arsenal ta dauka Ben White ya kamu da annobar a makon jiya, ya kuma killace kan sa, ba zai yi karawar ta ranar Laraba ba.

'Yan wasan da suka koma atisaye a Arsenal kawo yanzu sun hada da Hector Bellerin da Gabriel Magalhaes da Kieran Tierney da kuma Gabriel Martinelli.

Sai dai kungiyar ta Emirates ta ce Thomas Partey ba zai koma atisaye ba sai cikin watan Agusta, tana kuma sa ran Eddie Nketiah zai koma motsa jiki a cikin watan Satumba.