Arsenal ta ɗauki Martin Odegaard daga Real Madrid kan £30m

Arsenal ta kammala daukar ɗan wasan tsakiyar Martin Odegaard daga Real Madrid kan kudi fam miliyan 30, yayin da mai tsaron ragar da ta saya daga Sheffield United ya kammala koma wa kungiyar.

Dan kasar Norway mai shekara 22, ya shafe rabin kakar da ta gabata a matsayin aro a Arsenal.

Ya bugawa kungiyar wasa 20 a duka gasar da ya buga ya kuma ci kwallo biyu.

Shi kuwa dan wasan Ingila na 'yan kasa da shekara 21 Ramsdale ya buga wasan 38 a kakar wasanni da ta gabata a Premier.

Zai bi sahun Bernd Leno da Runar Alex Runarsson a matsayin gololin kungiyar.

"Akwai wasu 'yan abubuwa da zai sanya wa hannu, amma dai an gama duba lafiyarsa, wasu abubuwa ne da za mu kammala da Sheffield," in ji kocin Arsenal Mikel Arteta.

"Aaron matashin dan wasa ne mai hazaka kuma ya buga wa kasarsa wasan kasa da kasa. Zuwansa zai iya haifar da rige-rige tsakanin gololin da muke da su, kuma haka muke son gani domin su yi kokari - ko wanne hannu ya zama ana gogayya a cikinsa."

Odegaard zai haɗu da Ben White da Albert Sambi Lokonga da kuma Nuno Tavares wadanda Arsenal ta ɗauka a wannan karon.

Ba zai buga wasan Premier ba da za ta buda ranar Lahadi da Chelsea har sai an ba shi biza.

An tambaye shi wace gudunmuwa Odegaard zai bayar a cikin tawagar Arsenal sai Arteta ya ce: "Ya kawo mana sauye-sauye masu yawa a bara, ya sauya kungiyarmu zuwa yanayi mai kyau, muna bukatar masu kwakwalwa da yawa a kungiyarmu.

"Har yanzu matashi ne ya san kungiyar sosai, yana kuma da kwakwalwa irin wadda muke nema."

Dan wasan Norway din ya koma Real Madrid ne a Stromsgodset a 2015 amma wasa takwas kawai ya buga wa kungiyar ta Sifaniya.