Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Marcus Rashford: Dan kwallon Ingila ya koma yin atisaye a Manchester United
Dan wasan Manchester United, Marcus Rashford ya koma karbar horo a sansanin kungiyar da ke Carrington.
Kocin United, Ole Gunnar Solskjaer ya ce dan kwallon na murmurewa daga aikin da likitoci suka yi masa a raunin da ya ji a kafada
Dan wasan tawagar Ingila ya fada a makon jiya cewar likitoci sun yi nasarar yi masa tiyata a kafada a raunin da ya ji a lokacin atisayen tun kan fara kakar bana.
Raunin ne ya bai wa dan kwallon mai shekara 23 cikas da bai buga wa tawagar Ingila karawa da yawa a Euro 2020 ba, wanda ya barar da fenariti a wasan karshe da Italiya a Wembley.
Bayan da ya ji raunin Solskjaer bai fayyace lokacin da zai yi jinya ba, illa dai wasu jaridun Birtaniya sun yanke wa'adin mako 12, kafin ya koma taka leda.
Ranar Asabar Manchester United ta tashi 1-1 a gidan Southampton a wasan mako na biyu da fara Premier League kakar 2021-22 a St Mary.