Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mohamed Sala: Liverpool za ta tsawaita yarjejeniyar dan kwallon Masar
Jurgen Klopp ya ce Liverpool tana tattaunawa da Mohamed Salah, domin tsawaita yarjejeniyar ci gaba da zama a Anfield.
Salah wanda ya koma Liverpool daga Roma a 2017, yana da sauran kwantiragin kaka biyu a Anfield.
Dan wasan tawagar Masar ya ci kwallo 126 a dukkan fafatawar da ya yi wa Liverpool har da lashe Premier League da kuma Champions League.
Ranar Asabar Salah, wanda ya ci kwallo 98 a wasa 158, ya buga karawar da Liverpool ta doke Burnley 2-0 a wasan mako na biyu a Premier League ta bana.
Diego Jota da kuma Sadio Mane ne suka ci mata kwallayen da ta hada maki ukun da take bukata a fafatawar ta Asabar a Premier League.
Ranar Asabar 14 ga watan Agusta, Liverpool ta je ta doke Norwich City da ci 3-0 a wasan makon farko a Premier League a Carrow Road.
A baya-bayan nan Liverpool ta tsawaita kwantiragin 'yan wasa a Anfield da suka hada da Fabinho da Alisson da Virgil van Dijk da kuma Trent Alexander-Arnold,
Klopp ya kuma ce kyaftin din kungiyar Jordan Henderson na daf da saka hannu kan yarjejeniyar tsawaita zaman sa a Liverpool.