'Yan wasan Barcelona 23 da suka je Bilbao buga La Liga

Barcelona ta ziyarci Athletic Bilbao, domin buga wasan mako na biyu a gasar La Liga ranar Asabar.

Wannan shine wasan farko da kungiyar Camp Nou za ta yi a wajen, bayan da ta doke Real Sociedad 4-2 ranar Lahadi 15 ga watan Agusta.

Ita kuwa Athletic Bilaboa zuwa ta yi Elche ta tashi 0-0 ranar Litinin 16 ga watan Agusta.

Tuni kocin Barcelona, Ronald Koeman ya bayyana 'yan wasa 23 da ya je da su Bilbao domin buga karawar ta ranar Asabar.

Cikin su sun hada da Dest da Pique da R. Araujo da Sergio da Riqui Puig da Griezmann da Memphis da Braithwaite da Neto da R. Manaj da Lenglet da kuma Pedri.

Sauran sun hada da Jordi Alba da S. Roberto da F. De Jong da E. Royal da Eric da Inaki Pena da Demir da Nico da Gavi da Balde da kuma Arnau Tenas.

Waso 10 baya da Barcelona ta buga a gidan Bilbao:

  • 2011: Athletic 2-2 Barça
  • 2013: Athletic 2-2 Barça
  • 2013: Athletic 1-0 Barça
  • 2015: Athletic 2-5 Barça
  • 2015: Athletic 0-1 Barça
  • 2016: Athletic 0-1 Barça
  • 2017: Athletic 0-2 Barça
  • 2019: Athletic 0-0 Barça
  • 2019: Athletic 1-0 Barça
  • 2021: Athletic 2-3 Barça

Tun daga 2011 Athletic Bilbao da Barcelona sun kara sai 41 a dukkan fafatawa, Barcelona ta ci 28, Bilbao ta yi nasara a biyar da canjaras takwas.

Ranar Juma'a Ronald Koeman ya ja ragamar atisaye, inda mai tsaron raga Marc ter Stegen ya shiga cikin 'yan wasan, amma likitoci ba su bayar da izinin ya taka leda ba a Bilbao.

Karo na biyu kenan da Barcelona za ta yi wasa a La Liga ba tare da Lionel Messi ba, wanda ya yi kaka 21 a kungiyar.

Messi ya koma Paris St Germain da taka leda, kawo yanzu bai fara yi mata tamaula ba, tun bayan da ya koma Faransa da taka leda a bana.

Kyftin din Argentina ya koma PSG bayan da Barcelona ta shiga matsin tattalin arziki, da ta kai bashi ya yi mata katutu.