Cristiano Ronaldo: Allegri ya ce dan wasan bai taba cewar zai bar Juventus ba

Cristiano Ronaldo "bai taba nuna alamar zai bar'' Juventus ba in ji kocin kungiyar Massimiliano Allegri.

A makon nan Ronaldo ya yi rubutu a kafar sa ta sada zumunta cewar rade-radin da ake kan zai bar Juventus ''rashin girmamawa ce a kanshi da kuma a matakin sa na dan kwallo.''

A wata hira da kocin Juventus, Allegri ya ce kyaftin din tawagar Portugal zai ci gaba da taka leda a Turin.

"Ronaldo bai taba nuna alamar zai barmu ba,'' ya fada min cewar zai ci gaba da taka leda a Juventus in ji Allegri.

Ranar Lahadi Juventus za ta ziyarci Udinese a wasan makon farko a gasar Serie A kakar 2021-22.

Ana ta yada jita-jitar cewar Ronaldo zai bar Juventus a bana, wasu rahotannin sun ce zai koma taka leda Real Madrid ko Paris St-Germain ko kuma Manchester City.

Sai dai ranar Talata, kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti ya yi watsi da batun cewar Ronaldo zai sake komawa Sifaniya a karo na biyu.

Tsohon dan kwallon Manchester United ya koma Juventus daga Madrid kan fam miliyan 99.2 a 2018.

A cikin watan Mayu ya zama dan wasan da ya ci kwallo 100 da wuri a Juventus a fafatawa 131 da ya yi.

Saura wata 10 kwantiragin Ronaldo, wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or karo biyar jumulla ya kare a Juventus,