John Stones: Dan wasan Ingila ya tsawaita yarjejeniyar kaka biyar a Manchester City

John Stones

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dan kwallon Ingila ya yi wa Manchester wasa 35 a dukkan karawa a kakar da ta wuce

Mai tsaron bayan Manchester City, John Stones ya tsawaita yarjejeniyar kaka biyar, domin ya ci gaba da taka leda a kungiyar da ke rike da kofin Premier League.

Tun farko kwantiraginsa za ta kare a karshen kakar badi, yanzu zai ci gaba da murza leda a City har zuwa karshen kakar 2026.

Mai shekara 27, ya taka rawar da ta kai City ta lashe Premier League da aka kammala, yana cikin 'yan kwallon Ingila da suka kai tawagar wasan karshe a Euro 2020.

A baya an yi hasashen zai bar Etihad, bayan da Aymeric Laporte da kuma Ruben Dias suka sha gabansa a tsaron bayan kungiyar.

Stones da Dias sun fuskanci juna a tsaron bayan City a kakar da ta wuce, an kuma bayyana shi cikin 'yan wasan Premier League 11 a shekarar 2021.