Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Maddison, Ronaldo, Kane, Lukaku, Abraham, Ibrahimovic, Coady, Kounde

James Maddison

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Gunners tana jan kafa wajen biyan £60m da aka sanya kan dan wasa Maddison

Arsenal ta nemi daukar dan wasan tsakiyar Leicester City da Ingila James Maddison. An ce Gunners tana jan kafa wajen biyan £60m da aka sanya kan dan wasan mai shekara 24, don haka za ta bayar da wani dan wasanta a matsayin wani bangare na yarjejeniyar. (football.london)

Manchester City ta amince ta biya £130m kan dan wasan Tottenham da Ingila Harry Kane, mai shekara 27, kuma tana da kwarin gwiwar cewa za a amince da tayinta. (Athletic, subscription required)

Inter Milan za ta amince ta karbi £100m daga Chelsea ba don tana so ba kan dan wasan Belgium Romelu Lukaku, mai shekara 28, bayan jami'ai a kungiyar sun bayyana a asirce cewa suna son sayar da babban dan wasa domin samun kudin gudanar da wasu ayyukansu. (Metro)

Sai dai bayanai sun nuna cewa Lukaku yana son komawa Chelsea saboda yana ganin bai gama cimma burinsa ba a Stamford Bridge. (Sun)

Cristiano Ronaldo

Asalin hoton, Getty Images

Har yanzu dan wasan Portugal Cristiano Ronaldo yana son barin Juventus domin tafiya Real Madrid, sai dai dan wasan mai shekara 36 yana sane cewa damarsa ta komawa Bernabeu ta dogara ne da nasara ko rashin nasarar Juve ta daukar dan wasan Paris St-Germain mai shekara 22 dan kasar Faransa Kylian Mbappe. (AS - in Spanish)

Dan wasa Sifaniya Aymeric Laporte ya bayyana wa Manchester City karara cewa yana son tafiya La Liga a bazarar da muke ciki, inda ake sa ran dan wasan mai shekara 27 zai je Barcelona ko Real Madrid. (90min)

Southampton da West Ham suna son daukar dan wasan Nice da Austria mai buga gasar Under-21 Flavius Daniliuc, mai shekara 20. (Mail)

Liverpool, tare da wasu kungiyoyin Gasar Firimiya da ba a ambaci sunayensu ba, suna son daukar dan wasanBournemouth dan kasar Netherlands Arnaut Danjuma, mai shekara 24, wanda tuni Villarreal ta nemi daukarsa.An ceBournemouthtana son karbar kusan £21.5m kan dan wasan. (Marca - in Spanish)

Aston Villa ta na fatan kulla yarjejeniya da dan wasan Chelsea da Ingila Tammy Abraham, mai shekara 23, da tsohon dan wasan da ke buga wa Ingila Gasar 'yan kasa da shekara 21 kuma dan wasan Manchester United Axel Tuanzebe, mai shekara 23. Dukkan 'yan wasan biyu sun taba yin zaman aro a Villa Park kuma sun taimaka wa kungiyar ta samu ci gaba a Gasar Firimiyar 2018-19. (Telegraph - subscription required)

Chelsea ta bayar da dan wasan Brazil mai shekara 25 Kenedy ga Sevilla a wani bangare na daukar dan wasa mai shekara 22 Jules Kounde bayan tun da farko ta bayar da dan uwansa dan kasar Faransa Kurt Zouma, mai shekara 26, a bangaren yarjejeniyar. (Sun)