Romelu Lukaku: Inter ta ki sallama tayin da Chelsea ta yi wa dan wasan Belgium

Asalin hoton, Getty Images
Inter Milan ba ta sallama tayin fam miliyan 85 da Chelsea ta yi wa Romelu Lukaku ba.
Lukaku, mai shekara 28, shine kan gaba da Chelsea ke son daukar mai cin kwallaye, bayan da Borussia Dortmund ta ce ba za ta sayar da Erling Braut Haaland a kakar nan ba.
Duk da dai Inter Milan na fama da matsalar tattalin arziki, amma tana fatan rike dan kwallon tawagar Belgium din.
Lukaku tsohon dan kwallon Chelsea, yana daga cikin kashin bayan Inter, wadda ta lashe Serie A a kakar da ta wuce, kuma karon farko tun bayan 2010.
Chelsea tana kuma da niyar bai wa Inter Milan, Marco Alonso cikin kunshin yarjejeniyar da take fatan za su kulla.
Lukaku ya buga karawa 15 a lokacin da ya yi kaka uku a Chelsea tsakanin 2011 da 2014, daga baya ta sayar wa Eveton dan kwallon, bayan da ya taka rawar gani a wasannin aro da ya buga wa kungiyar.
Kadan ya rage ya sake komawa Chelsea a 2017, sai ya zabi aiki tare da Jose Mourinho a Manchester United da ta saya kan fam miliyan 75.
Lukaku ya ci kwallo 42 a wasa 96 da ya yi wa United, sannan Inter ta saye shi a 2019 kan fam miliyan 74 a matakin wanda ta dauka mafi tsada a taruhin kungiyar.











