Marcus Rashford: Dan kwallon Man United zai yi jinyar wata biyu

Marcus Rashford

Asalin hoton, Getty Images

Dan wasan Manchester United, Marcus Rashford ba zai taka leda ba har sai karshen Oktoba, bayan da za a yi masa aiki a raunin da ya yi a kafada.

Ranar Talata likitoci suka auna koshin lafiyar Rashford, mai shekara 23, wanda ya yi fama da radadin ciwon a kakar 2020/21.

Hakan ne ya sa United ta yanke shawarar da likitoci suyi masa aiki, domin ya samu fuskantar kalubalen kaka mai zuwa.

Sai dai kuma aikin ba zai samu ba har sai karshen watan Yuli a lokacin ne likitan zai samu dama, saboda abubuwan da ke gabansa.

Ana sa ran Rashford zai yi jinyar mako 12, wanda hakan koma baya ce ga Ole Gunnar Solskjaer, wanda ke shirin ganin ya taka rawar gani a kakar da za a fara cikin watan Agusta.

Wannan labarin ya fito ne kwana daya, bayan da likitoci suka auna koshin lafiyar Jadon Sancho, wanda zai kammala komawa United daga Borussia Dortmund kan fam miliyan 73.

Rashford ya ci kwallo 11 a karawa 37 a Premier League da ta wuce, amma bai taka rawar gani ba a gasar cin kofin nahiyar Turai ta Euro 2020 da Italiya ta lashe.

Ya buga wa tawagar Ingila wasa biyar a Euro 2020, yana daga cikin 'yan kwallo ukun da suka kasa ci wa kasar fenariti a karawar karshe ranar Lahadi a Wembley.

Rashford da Jadon Sancho da kuma Bukayo Saka, sun yi ta samun kalaman cin zarafi a kafar sada zumunta, sakamakon kasa cin daga kai sai mai tsaron raga da suka yi.

Rabonda tawagar Ingila ta kai wasan karshe a babbar gasar tamaula tun 1966, bayan da ta lashe kofin duniya.